Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Sanatan Amurka Lindsey Graham ya fada a wata hira da gidan talabijin na NBC cewa, wannan kalar mamayar ce kawai zata gamsar da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Tel Aviv ta yanke shawarar cewa ba za ta iya cimma burinta ba ta hanyar kawo karshen yakin da ta ke yi Hamas ba domin tana neman cikakken ikon Gaza ne.
Sanatan na Amurka ya kara da cewa Washington ta yi imanin cewa babu yadda za a yi a tattauna don kawo karshen yakin da Hamas ke yi.
Bisa rahoton Kamfanin ISNA ya cewa, Graham yayin da yake ishara da shirin da ake zargin yahudawan sahyoniya ke yi a zirin Gaza ya ce: Suna son su yi a Gaza abin da muka yi a biranen Tokyo da Berlin, wato mu karbe iko da karfin tuwo, sannan kuma a fara da samar da makoma mai kyau ga Falasdinawa, da fatan cewa Larabawa za su mamaye yammacin kogin Jordan da Gaza.
Ya yi iƙirarin: "Ina tsammanin za a iya samun mutane a Hamas da za su amince da wucewa lafiya idan an saki fursunonin." Kuma ya ba da shawarar cewa ya kamata Isra'ila ta yi wannan tayin.
A ci gaba da da'awarsa ba tare da ambaton shiga tsakani da cin zarafi na gwamnatin sahyoniyawa da kuma barnar da ta yi a Gaza ba, Graham ya kara da cewa: Muddin kungiyar Hamas ta wanzu to babu wata makoma ga al'ummar Palasdinu, don haka abin da zan iya cewa shi ne, ina ganin a cikin kwanaki da makonni masu zuwa za ku ga wani yunkuri na soji na ruguza Hamas, kwatankwacin abin da muka yi a Tokyo da Berlin domin murkushe 'yan Nazi da Japanawa.
A cikin 'yan kwanakin nan, Steve Witkoff wakilin shugaban Amurka Donald Trump na musamman kan yankin Gabas ta Tsakiya, ya ce Washington na shirin mayar da tawagar masu tattaunawa zuwa Amurka domin tuntubar juna.
Tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnatin Isra'ila da Hamas ta ci tura saboda bukatu masu karo da juna kan yadda za a kawo karshen yakin. Hamas ta dage kan janyewar Isra'ila gaba daya daga Gaza. Tel Aviv dai ta ki kawo karshen fadan da take yi har sai Hamas ta mika mulki tare da mika makamanta.
Your Comment