19 Yuli 2025 - 21:34
Source: ABNA24
Jaridar Lebanon: Amurka Da Saudiya Na Neman Juyin Mulkin Ruwan Sanyi Don Sauya Ma'aunan Iko A Lebanon

Wata jaridar Lebanon ta rubuta cewa: Washington da Riyadh na neman juyin mulki ba tare da zubar da jini ba don sauya ma'auni na iko a Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran Ahlulbaiti (AS) ya habarta cewa: Radwan Al-Dheeb manazarci dan kasar Lebanon ya yi ishara da wannan batu cewa: An fitar da sabbin tsare-tsare a yankin musamman Siriya da Labanon a matakin farko, sannan kasashen Jordan da Iraki, wadanda babban burinsu shi ne binne yarjejeniyar Sykes-Picot da samar da kasashen kabilanci ga marasa rinjaye na Druze, Kurdawa da Alawiyawa. Ana aiwatar da wannan shiri tare da cikakken goyon bayan Amurka, rufe idon Turai da rashin taimakon Larabawa, kuma zai haifar da mummunan sakamako ga yankin Levant wato Shamat, wanda zai anfanar da Isra'ila. Gudanar da wannan fayil alhaki ne daya doru akan jakadan Amurka a Turkiyya, Tom Brick.

Dangane da wannan batu, kasar Labanon tana fuskantar kalubale da barazana mai girma da ke barazana ga wanzuwar kasar, to sai dai bangaren siyasar kasar Labanon na daukar wadannan al'amurra ba da muhimmanci ba da nuna halin ko-in-kula, kamar yadda ya tabbata a zaman majalisar dokokin kasar mai cike da ban haushi da bai ja hankalin al'ummar kasar ba.

A halin da ake ciki dai Amurka da Saudiyya na ci gaba da kokarin  haifar da wani juyin mulki a kasar Labanon; manufar ita ce a sauya ma'auni na madafun iko a kasar. Wadannan yunƙurin sun haɗa da shirin samun rinjayen 'yan majalisar dokoki a zaɓen da za a yi a watan Mayu mai zuwa, wanda ta inda za su iya tafiyar da ƙasar a ƙarƙashin yanayi da tsari na ƙasashen waje.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha