ABNA24 : Kungiyar agaji ta “Red Cross” ta sanar da aikewa da magunguna da sauran kayan aikin likitanci a cikin manyan motoci bakwai saboda a taimakawa mutanen da adadinsu ya kai 400 da su ka jikkata a birnin Mekele.
Shugaban kungiyar ta agaji a nahiyar Afirka Patric Yossef, ya ce magungunan da aka aike za su taimaka matuka wajen aikin da likitoci su ke yin a ceton rayuka a cikin birnin na Mekele.
Gwamnatin Habasha dai ta dauki tsauraran matakai na shiga cikin birnin Mekele tun da rikici ya barke.
342/