14 Nuwamba 2020 - 11:16
MDD: Akwai Yiyuwar A Tafka Laifuffukan Yaki A Rikcin Da Ke Gudanaa A Yankin Tigray Na Habasha

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar akwai yiyuwar rikicin da ke gudana a halin yanzu tsakanin dakarun gwamnatin Habasha da na ‘yan tawayen yankin Tigray na iya kazamta sosai da kuma yiyuwar tafka laiffuffukan yaki.

ABNA24 : Kakakin shugabar hukumar kare hakkokin bil’adama ta MDD, Michelle Bachelet, ya sanar da hakan inda ya ce: Akwai yiyuwar rikicin da ke gudanar zai kara kazamnta ainun da zai kai ga yin gagarumar hasarori da kuma rasa rayuka masu bugu da kari kan tarwatsa wani adadi mai yawa na mutane daga muhallansu.

Har ila yau jami’ar ta MDD ta ci gaba da cewa idan har rahoton da kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International ta fitar na irin kisan gillan da ake yi wa fararen hula ya tabbata, to hakan yana iya zama laifin yaki.

Rahotanni dai sun ce ya zuwa yanzu dai daruruwan mutane ne suka mutu kana wasu dubbai kuma suka gudu suka bar muhallinsu da tafiya gudun hijira zuwa kasar Sudan sakamakon wannan yaki na kwanaki 10 da ke faruwa tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawayen yankin Tigray din.

Gwamnatin Firayi ministan Abiy Ahmed dai sun ce dakarun jam’iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF) da ke rike da yankin ne suka fara kai hare-hare kan sansanonin sojin gwamnatin Tarayyar da ke yankin na Tigray da nufin kwasar makamai inda suka kashe wasu sojojin lamarin da gwamnatin tarayyar tace ba za ta amince da shi ba, don haka ta tura dakarunta yankin don ladabtar da su.

342/