ABNA24 : Wakiliyar MDD ta musamman a kasar Libya Stephanie Willams ce ta sanar da hakan a wani taron manema labaru ta hanyar bidiyo daga nesa, tana mai cewa masu halartar taron sulhun wanda MDD ke kula da shi a Tunisiya, sun amince da a gudanar da manyan zabuka a kasar a ranar 24 ga watan Disamba na 2021.
Williams ta kara da cewa; Ranar yin zaben za ta kasance mai matukar muhimmanci ga al’ummar Libya, domin za su sake tabbatar da halarcin cibiyoyin kasar.
Wakiliyar MDD a kasar Libya ta kuma ce; Al’ummar Libya sun ki jinin yadda baki ‘yan waje su ke tsoma baki a harkokin cikin gidansu, don haka suke son sake rike akalar tafiyar da al’amurran kasar tasu da kansu.
Wannan ita ce sanarwa mafi muhimmanci da ta fito daga taron sulhu na kungiyoyin kasar Libya da ake yi a kasar Tunisiya.
342/