2 Nuwamba 2020 - 14:38
Mutanen Kasar Aljeriya Sun Kauracewa Kuri’ar Raba Gardama Akan Tsarin Mulkin Kasar

A jiya Lahadi ne aka gudanar da kuri’ar raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar ta Aljeriya, amma ba a sami fitowar mutane masu yawa ba.

ABNA24 : Shugaban hukumar zaben kasar ta Aljeriya da ta shirya kada kuri’ar raba gardamar, Muhammad Sharafi ya bayyana cewa; adadin wadanda su ka kada kuri’ar bai wuce kaso 23. 7 % ba, da hakan yake nufin mutane miliyan 5.5 daga tsakanin mutane miliyan 32.5 da su ka cancanci kada kuria.

A yayin zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disamba na 2019 da ya dora shugaba Tabun akan mulki wadanda su ka kada kuri’ar sun kai kaso 39.93, wacce a wancan lokacin ma aka dauke ta mafi rauni.

An kada kuri’ar ne dai adaidai lokacin da shugaban kasar ta Aljeriya Tabun yake jiyya a kasar Jamus.

342/