A ranar Alhamis ne dai majalisar ta shirya karbar hujojin da Ambasada James Entwistle ya ce yana da su, wadanda ke nuna cewa 'yan majalisar sun nemi karuwai a kasarsa a watan Mayu.
Amma jakadan ya ki bayyana a gaban majalisar bisa hujjar cewa yana da rigar kariya, sai dai idan shi ya so yin hakan bisa radin kansa.
Shi ma dai ministan harkokin wajen Najeriyar da aka tsara zai bayyana tare da Mista Entwistle bai samu bayyana ba saboda yana kan wata ziyara a birnin Kigali na kasar Rwanda.288