1 Afirilu 2016 - 15:30
Gwarazan mu Shahidan Mu - An yi jana'izar Shahid Abbas Ishaq a Kaduna

A jiya Alhamis da yamma ne aka gabatar da jana'izar daya daga cikin shahidan mu,Shahid Abbas Ishaq a Markaz din 'yan uwa musulmi dake Tudun Wada Kaduna. Jana'izar ta wannan babban Shahidi namu tazo ne a jiya bayan shafe watanni uku da cikawar sa a gidan Kaso na Kaduna.

Sojoji sun kama Shahid Abbas Ishaq ne dan shekaru49 da haihuwa a Gyallesu gidan Sheikh El-Zakzaky suka kawo su gidan kaso na Kaduna alhali yana da raunuka na harsasai a jikin sa, saboda rashin kula da raunukam jikin sa da zubar jini ya cika a gidan Kason, bayan makwanni biyu da kawo su.

Tun daga wancan lokacin ake ta fafutukan karban gawar sa, sai a jiya ne aka mikawa dangin sa gawan inda aka yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Malam Aliyu Tirmizi ne ya jagoranci dimbin al'ummar musulmi a lokacin sallar jana'izar.288