25 Janairu 2016 - 16:02

Rahotanni daga Kamaru sun ce wasu 'yan mata 'yan kunar-bakin-wake sun tayar da bama-bamai uku a garin Bodo, da ke kusa da kan iyaka da Najeriya.

An tashi biyu daga cikin bama-baman ne dai a kasuwar garin, wacce ke cike makil da jama'a.

Har yanzu dai babu cikakken bayani a kan yawan mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren, kuma har yanzu hukumomi ba su ce komai ba game da harin.288