[Enter Post Title Here]
Manzon Allah (saaw) yace a cikin Mustadrikul Wasa’il,wato Mustadriku Wasa’ilush Shi’ah,cewa : “INNA LI QATLIL HUSAIN HARARATAN FI QULUBIL MU’UMININA LA TABRADU ABADAN”ma’ana Hakika kashe Husain (as) yana da wani dumi wato wani zafi a cikin zukatan Mu’uminai wanda ba zai yi sanyi ba (shi dumin )har abada.Wannan a cikin Mustadrikul Wasa’il wato littafan mu na Shi’a.Ya riga ya tabbata mana saboda haka bahasi akan isnadi ya kare,bahasi akan matani ya kare,bahasi akan dilalah na matani shi ma ya kare,mun tabbata kad’an cewa Manzon Allah (saaw) ya fadi haka,sannan waqi’in yanayin Mu’uminai ya tabbatar da hadisin daga shi Manzon Allah (saaw) .Wato duk lokacin da aka ambaci al’amarin Husain (as) sai ya zama MASHA’IR da AWAADIF na mutane sun motsa kamar kace yanzu al’amarin ya faru,shi wannan babban Shaahidi ne akan tabbatar gangarowan wannan hadisin daga Manzon Allah (saaw) da sharadin imani,amma in mutum yana daga cikin Nawasib irin wadannan Masha’ir din da Awaadif din za su taso amma ta jiha MU’AKKISA wal iyazu billah,zai zama yana samun ISHMI’IZAZ kamar yanda Allah Subhanahu wa Ta’ala Yake fadi tsigan jikin su zata dinga tashi idan ana ambaton Husain da Ahlul Bait da Manzon Allah (saaw),amma su Mu’uminai akan haddin ta’abirin Manzon Allah (saaw)su sukan yi mu’amala tare da waqi’a din DAF ko Karbala,wannan akan asasin bibiyan gurabu na shi Manzon Allah (saaw) umuman dangane da kuka akan matacce musamman in mataccen ya kasance AZIZ wato ya kasance mai daraja,wannan wani abu ne wanda yake tabbatacce a Masaadir din Musulmai,sannan yake tabbatacce a sirah din musulmai banda wanda yayi shuzuz wanda wannan shine Bawahabiyye kuma Basalafe,shi kuma wannan ba ma mashi wazani,sabanin shi bai da tasiri a wannan mas’ala din kuma gamsar da shi yana kusa ya zama mustahili.Amma in ba haka ba ta tabbata a wurare dabam dabam ko da a taqaice dangane da MASHA’IR. Na farko ya kamata mutane su sani in basu sani ba cewa Manzon Allah (saaw) gabaki dayan shi Adifa ne,Manzon Allah (saaw) gabaki dayan shi Masha’ir ne wato SHU’UR ne,wato Manzon Allah (saaw) gabaki dayan shi fadaka ne da hudur ba gafla a tattare da shi (saaw)asasan.Wato shi mutum ne da mafi cikan ma’anar kalmar mutum wanda yake mu’amala tare da waqi’I a mafi koluluwan mustawa,sannan akan asasin hikma,Manzon Allah yana yin kuka,sannan yana nuna damuwa kuma yana nuna farin ciki. Yazo akan cewa a ranar Uhud a lokacin da dukkan mutane gabaki daya suka ga kukan Manzon Allah (saaw) a yakin Uhud,sun shedi kukan Manzon Allah a lokacin da ya ga zakin Allah kuma zakin shi kamar yanda Ibn AbdulBar daga cikin malaman Sunnah ba malaman Shi’ah ba.Ibn AbdulBar ya fadi a cikin Al-Isti’ab din shi a lokacin da yake tarjaman Hamzah (as) ammin Manzon Allah (saaw) yace “A LOKACIN DA MANZON ALLAH YA GA HAMZAH A KASHE SAI YAYI KUKA,AMMA DA YA MATSA KUSA DA SHI SAI YA GA AN YI MASHI MASALU TO A LOKACIN SAI YA SIDE YA SUMA”.Irin abin da Yan DAESH suka gada daga Hind kenan kamar yanda tayi ma Hamzah (as),wato lokacin da Hind Akilatul Akbad wadda ta sunnatawa Daulatul Islam fil Iraq wash Sham ko Islamic State of Iraq and Syria,to wannan abin da Manzon Allah ya gani ya sa ya side ya suma ya fita daga cikin yanayin shi Ad-dabi’iy,wannan daya kenan. Sannan Al-Waqidiy daga cikin manya manyan malaman tarihi na Sunnah kamar yanda yake a cikin juz’I na 15 na sharhin Nahjul Balagah na Ibn Abil Hadid Al-Mu’utaziliy As-Sunniy yake cewa: “MANZON ALLAH (SAAW) YA KASANCE A WANNAN RANAN (ranar Uhud ) IDAN SAFIYYAH TAYI KUKA SHIMA ALBARKACIN KUKAN TA SAI YAYI KUKA,HAKA AZZAHRA (AS) TA KASANCE TANA KUKA LOKACIN DA MANZON ALLAH (SAAW) YAYI KUKA AKAN HAMZAH (AS)”.Sannan ranar da Manzon Allah (saaw) yayi ta’aziyyan Zaid da Zul Janahain da Abdullahi bn Rawaha,Manzon Allah (saaw) a ran nan yayi kuka a lokacin da aka kashe su kamar yanda Al-Bukhari ya rawaito a Babin Jana’iz, ka duba ka gani. Sannan Ibn AbdulBar ya fadi a lokacin da yake tarjaman Zaid a cikin Al-Isti’ab,yana cewa : “MANZON ALLAH (SAAW)YAYI KUKA AKAN JA’AFAR AD-DAYYAR DA ZAID ,YACE DANGANE DA SU DIN –muka ce Manzon Allah dukkan shi Masha’ir ne sannan dukkan shi Awadif ne,in kana da fikran cewa Manzon Allah busashshe ne a zuciya ka tashi daga wannan fikra din a yau,dukkan shi rahama ne ,dukkan shi Shu’ur ne ,sannan dukkan shi Adifa – YAN UWA NA NE DUKKAN SU SU BIYUN (wato Ja’afar da Zaid)MASU KWANTAR MIN DA HANKALI NE MASU BANI LABARI. Yazo a Sahihul Bukhari cewa Manzon Allah yayi kuka ran da dansa Ibrahim ya rasu yayi kuka sai AbdurRahman bin Auf yake cewa “WAN ANTA YA RASULALLAH” ma’ana har kai ma kana kuka?(wannan ISTIGRAB ne da TA’AJJUB,wato yana mamaki Annabi yana kuka )sai Manzon Allah yace mashi “YA ABDARRAHMAN INNAHA RAHMA”ma’ana ya kai AbdurRahman jin kai ne wato tausayi ne,sai Manzon Allah ya bibiye wannan Kalmar da cewa “HAKIKA IDO YANA HAWAYE KUMA ZUCIYA TANA BAKIN CIKI AMMA DUK DA HAKA BA ZAMU CE BA SAI ABIN DA YAKE YARDAR DA UBANGIJIN MU, AMMA TABBAS MU DA RABUWA DA KAI YA IBRAHIM MUNA MASU BAKIN CIKI-wannan dabi’a ce ta dan Adam wanda ba zaka iya danne ta ba saidai in kana Basalafe ko Bawahabiye ko wanda ya tasirantu da hadisan da basu inganta ba,kuma koda suna cikin Bukhari ko Muslim,wanda kila mu kawo wasu daga cikin su,mu kuma yi Naqadin su insha ‘Allah .Sannan da yake ba ina so na kawo su da yawa bane,akwai inda shi Manzon Allah (saaw) yake cewa dangane da kuka “WANNAN RAHMA CE(hawayen) DA ALLAH YAKE SANYAWA A CIKIN ZUKATAN BAYIN SHI,KUMA ALLAH KAWAI YANA JIN KAN MASU JIN KAI NE DAGA BAYIN SHI (wannan Ka’ida ce).Sannan akwai abin da Al-Bukhari ya rawaito daga Ibn Umar cewa Sa’ad Ibn Abi Wakkas ya taba rashin lafiya sai Manzon Allah (saw) ya ziyarce shi tare da wata jama’a na Sahabban Sa sai Manzon Allah Ya sami Sa’ad din ya suma sai Yayi kuka saboda suman Sa’ad din,to a lokacin da mutane suka ga Yana kuka (Annabi)sai su ma suka yi kuka.Sannan Manzon Allah (saaw) Ya taba zuwa wurin ta’aziyan shi Ja’afar dan Abi Talib,sai Ya je wajen Asma’u bint Umais yayi ma ta ta’aziya sai ya same ta tana kuka,sai Azzahra ta shigo tana kuka tana cewa “WA AMMA”sai Manzon Allah (saw) yace “ALA MISLI JA’AFARIN FAL TABKIL BAWAKIN”-wannan jumla ce kalida ila yaumil kiyama-ma’ana akan irin Ja’afar to masu kuka su yi kuka –DILALA din a bayyane take ai,wannan umurni ni,a Usulu Fiqhi sunan wannan Umurni wato umurni daga Manzon Allah (saaw). Ya zo a cikin Ibn Jarir da Ibn Asir malaman tarihi da ma’abucin Al-Aqdul Farid da dukkan ma’abuta sirah,sannan Imam Ahmad bn Hambal tare dasu ya rawaito a cikin hadisin Ibn Umar a shafi na 40 a juz’I na 2 daga Musnad din shi cewa : “Manzon Allah (saaw) ya dawo daga Uhud,sai matan Ansarawa suka dinga kuka akan wadanda aka kashe daga mazajen su,sai Manzon Allah (saaw) Yace amma shi ko Hamzah ba masu yi mashi kuka –wato kenan kwadaitarwa da ba da umurni daga Manzon Allah ayi kuka ma wa wane ta fadin shi cewa amma shi Hamzah ba wanda yake yi mashi kuka –sai bayan nan Manzon Allah (saaw) Yayi bacci sai da Ya farka sai Ya samu suna yi wa shi Hamzah kuka,wato sun karbi umurnin Shi (saaw).Sai Imam Ahmad bn Hambal ya cigaba da cewa sai ya zama su matan Ansar tun daga ranar Uhud ya zama sunnah tsayayya a wajen su idan za su yi kuka ma wani wanda ya rasu sai su fara da Hamzah (as)(saboda bin umurnin Manzon Allah (saaw) ,wato har zuwa yau din ka kenan ).Wannan yana nuna kuka ya halatta in ba sunan ka Bawahabiye mai hiqdi da nasbu akan Manzon Allah (saaw) ba.Sannan kun san Ya’akub (as) yayi kuka akan danshi Yusuf ,shekara 80 yayi yana kuka,wato kenan muddar rabuwar shi da dan shi Yusuf(as),daga ran da ya faku har zuwa ran da suka hadu yana kuka,kuma Allah ya hikaito haka in da yake cewa “YA ASAFAA ALA YUSUFA WABYADDAT AINAAHU MINAL HUZNI FA HUWA KAZEEM “ma’ana ya bakin ciki na akan Yusuf sai ya zama idanun sa guda biyu sukai fari(me ye ma’anar idanun sa guda biyu suka yi fari ?wato sai ya makance saboda kuka)wato wannan retina ko kwayar bakin na idonsa ya koma fari,wato WABYADDAT AINAHU sai suka yi fari wato ya makance,shi yasa daga baya ya dayo masa da ganin shi wato IRTADDA BASIRAN ,Yusuf (as) Takwinan da Wilaya ya mai do mashi da ganin shi,wannan shi ma bahsi ne dabam.FA HUWA KAZEEM wato yana mai kunci saboda wannan bakin cikin na shekar 80 yana kuka akan Yusuf (as).Wannan haka Ibrahim (as),sannan in ka zo akan Husain (as),zaka ga farkon wanda ya fara kuka akan Husain (as) shine Manzon Allah (saaw) tun a lokacin waqi’an Karbala bata abku ba,wato ba a riga an zo shekara ta 60 bayan hijra ba amma Manzon Allah yayi mashi kuka daga littafan Ahlus Sunnah Wal Jama’a, ba zamu kawo rawayoyin Shi’a ba amma zamu kawo na Sunnah kawai . Yazo daga Musnad din Imam Ahmad bn Hambal daga Hadisin Ali (as) shafi 85 a juz’I na 1 da isnadi daga Abdullahi bn Najar daga Mahaifin shi cewa “YAYI TAFIYA TARE DA ALI (AS) WATA RANA,LOKACIN DA IMAM ALI (AS) YA DUMFARI NAINAWA (wato kasar Karbala),A LOKACIN ZAI JE YAKIN SIFFIN A IRAQ,SAI AKA JI SHI YANA KIRA YANA CEWA KA DAURE YA ABA ABDILLAH (wato Husain )-a lokacin Husain yana da rai –DAURE YA ABA ABDILLAH A GABAR FURAT,SAI SHI MAI RIWAYAR YACE MENENE WANNAN ABIN DA KAKE FADI,SAI YACE :NA TABA ZUWA MANZON ALLAH (SAAW)WATA RANA ALHALI A LOKACI IDANUN SA SUNA KWARARA (wato yana kuka)SAI NACE(wato ni Ali kenan ):YA MANZON ALLAH MENENE LABARIN IDANUN KA?SAI YACE JIBRIL NE DATSU YA TASHI DAGA NAN WURI NA TO SAI YA BANI LABARI CEWA DANA ZA A KASHE SHI A GABAR FURAT,SAI JIBRIL DIN YACE MIN :KANA SO IN BAKA DAGA TURBA DIN SHI ,SAI NACE MASHI EE ,SAI JIBRIL YA MIKA HANNAYEN SHI YA DAMKO WATA DAMKA DAGA TURBAYA DAGA KARBALA ALHALI SUNA MADINA –wannan su ake ce ma hadisan Dayyul Ard,shi ma kuma bahsi ne daban-SAI YA BANI ITA IN JI MANZON ALLAH SABODA SAI NA KASA RIKE IDANU NA SUKA DIN GA KWARARA.Kenan farkon mai kuka akan Husain shine Manzon Allah daga Ahmad bn Hanbal da sauran Malaman Sunnah. Ibn Sa’ad ya rawaito a cikin Dabaqat din shi,kamar yanda yake a Sawa’iqul Muhriqa na Ibn Hajr Al-Haisami daga Sha’abi cewa ‘’ALI (AS) YA TABA WUCEWA WATA RANA TA KARBALA A LOKACIN ZAI TAFI YAKIN SIFFIN,SAI YAZO KUSA DA NAINAWA ,SAI ALI YA TSAYA,SAI YA TAMBAYI YA SUNAN WANNAN GURIN –ba wai bai sani bane-SAI AKA CE MASHI KARBALA ,SAI YAYI KUKA HAR SAI DA YA JIKA KASA DA HAWAYEN SHI,SAI YACE (Ali (as))-wato ya fara bada labari-NA SHIGA WA MANZON ALLAH (SAAW) LOKACIN YANA KUKA SAI NACE :ME YAKE KUKANTAR DA KAI ?MAHAIFINA DA MAHAIFIYA TA SU ZAMA FANSA GARE KA,SAI YACE MALA’IKA JIBRILU YA ZO MIN DATSU YA NA BANI LABARI….har karshen hadisin. Mawardi Ash-Shafi’iy a babin Inzarun Nabiy bima Sayahdisu ba’adi ma’ana a babin gargadin Manzon Allah akan abin da sai faru a bayan shi,wato MUGAYYABAT MUSTAQBALIYYA wanda yake bada labarin su daga littafin shi A’ALAMUN NUBUWWAH daga Urwa daga Ummul Mu’uminina A’isha take cewa :HUSAIN (AS) YA SHIGO MA MANZON ALLAH (SAAW) ANA LOKACIN ANA YI WA MANZON ALLAH WAHAYI ,SAI JIBRA’IL (AS) YACE AL’UMMAR KA ZATA FITINU BAYAN KA TA KASHE WANNAN DAN NAKA BAYAN KA SAI JIBRIL DIN YA SANYA HANNAYEN SA SAI BASHI KASA DAGA KARBALA DIN KENAN,A WANNAN KASAR NE ZA A KASHE SHI,SUNAN KASAR DAF –shi yasa muke cewa WAQI’ATUL DAF wato itace Karbala –TO LOKACIN DA JIBRIL YA TAFI SAI MANZON ALLAH FITA ZUWA SAHABBAN SHI A WAJE-kila a ce a a zaure ko farfajiya ko whatever-ALHALI KASAN TANA HANNUN SHI,DAGA CIKIN SAHABBAN AKWAI ABUBAKAR DA UMAR DA ALI HUZAIFA DA USMAN DA ABU ZAR YANA KUKA,SAI SUKA CE:ME YAKE KUKANTAR DAKAI YA MANZON ALLAH (SAAW)?SAI YACE JIBRIL YA BANI LABARI CEWA DANA HUSAIN ZA A KASHE SHI A BAYA NA A KASAR DAF ,YA ZO MIN DA WANNAN KASAR ,YA KUMA CE MIN MAKWANCIN SHI A NAN NE.Sannan akwai riwayoyin da suke nuni da Manzon Allah da yayi kuka Sahabban su ma suka yi kuka da kukan shi,wanda majlisin AZAH na farko kamar yanda suke cewa shine Manzon Allah(saaw). Akwai riwaya daga Imam Sadiq (as) wanda yake magana akan wadanda suke ziyartar kabarin Husain (AS) wanda shi ma Nawasib suna fada da wannan.Tun da daman zaman mu bahsosi ne to zaman mu na yau itace KADDARA kafin in zo wurin,akan Kaddara nake so in yi magana,wadannan shinfidu ne.Imam Sadiq (as) yana cewa kamar yanda ya zo a Kamiluz Ziyarat da kuma Al-Kafi na Kulaini da Shaikus Saduq a Sawabul A’amal,duka wadannan littafan mu ne,Imam Sadiq na cewa “YA ALLAH WANDA YA KEBANTA MU DA KARAMA YA KUMA YI MANA ALKWARIN CETO RANAR ALKIYAMA KUMA YA KEBANCE MU DA WASIYYA BAYAN MANZON SHI,YA BAMU ILIMIN ABIN DA YA WUCE DA ILIMIN ABIN DA YA RAGE,YA WANNAN WANDA YA SANYA ZUKATA DAGA CIKIN MUTANE SUNA KARKATOWA ZUWA GARE MU KA GAFARTA MIN,KA GAFARTA WA YAN UWANA (musulmi kenan ) KUMA KA GAFARTA MA MASU ZIYARTAR KABARIN KAKAN A HUSAIN (AS)-wannan ya rage naka kayi bincike ya fadi wannan hadisin ko bai fadi ba saboda wannan ba muhallin bahsin shi bane amma mu ya tabbata mana ya fadi.Suna cewa Yan Shi’ah sun ce kasar Karbala tafi Madina da Makka,ko saboda gafla ko saboda hiqdi ko tauri kai ko saboda ta’assubanci ko saboda Nasbu,suna cewa Yan Shi’a suna cewa Karbala tafi Makka da Madina,daya kenan.Sannan suna cewa wai yan Shi’a sun ce ziyarar Husain tafi hajji sau kaza saboda sun ga riwayoyi daga littafan mu wadanda wasun su suna iya zama ingantattu kad’an amma basu fahimce su ba.Ba dole idan abu yana da lada mai yawa yana nuna matsayin shi kenan a wajen Allah.Sallar dare ya jama’a yana da yawa amma karshen hukuncin ta a cikin addini shine mustahab,in ka kashe dare kana sallar dare amma sai ba kayi sallar Asuba ba,wato kayi mustahab ka jefar da wajib,me kayi kenan?a hakkin mu ba akan hakkin Annabi ba,Sallar Asuba ta fi sallar dare amma zaka iya samun sallar dare tafi Asuba lada.In muka ce maka in ka je Karbala kana da ladan hajjin ishirin sai ka tambaye mu muyi maka bayani ko ?In kace mecece madogarar ku sai muce maka:Na farko ba muna nufin Hijjatul Islam ba wato ba Hajjin Wajib ba,akan wannan mizanin na Sallar dare da Sallar Asuba,ba muna nufin Hajjin wajibi ba wanda yake farilla ne akan mu tare da Istida’a.Sannan na biyu,yawan lada ba ya nuni akan fifiko kamar yanda ya tabbata wannan misalin.Sannan na uku ga wanda bai samu zuwa hajji ba,sannan sannan amma duka wadannan gabaki dayan su suna da amfani ne ga wanda yake da idraki amma ga nasibi basu da amfani saboda yana fakewa dasu ne domin yayi gaba kuma ba zai amsa ba balle ya fahimta-Sai Imam Sadiq din ya cigaba da cewa :WADANNAN WADANDA SUKA CIYAR DA DUKIYOYIN SU SUKA WAHALAR DA JIKUNAN SU DOMIN KWADAYIN SU YI MANA NAGARTA,KUMA DA SUKA YI WANNAN DOMIN KWADAYIN ABIN DA YAKE WAJEN KA YA ALLAH,TO ALLAH KA GAFARTA MASU ,WADANDA SUKA YI WANNAN ZIYARA DIN DOMIN SANYA FARIN CIKI A ZUCIYAR ANNABIN KA KUMA DOMIN AMSA KIRAN MU AKAN A RAYA AL’AMARIN MU KUMA KA GAFARTA MASU SABODA BAKIN CIKI DA KUNCI DA SUKA SANYA A CIKIN ZUKATAN MAKIYAN MU …….har karshe,kuma ga sunan kana ganin su a zahiri. Tab’an bayan kuka akan Husain (as)ana so ka wuce kukan kamar yanda muke fadi kullum.Manzon Allah(saaw) ya fadi cewa :INNA LI QATLIL HUSAIN HARARTAN FI QULUBIL MU’UMININ LA TABRADU ABADAN.Sannan Manzon Allah yace : “HUSAINUN MINNI WA ANA MIN HUSAIN ,AHABBALLAHU MAN AHABBA HUSAINA,HUSAINUN SIBDUN MIN ASBAD ma’ana Husain daga gare ni yake ni kuma daga Husain nake,Allah ka kaunaci wanda ya kaunaci Husain ,Husain jika ne daga cikin jikoki.Shi Al-Husain din da kanshi yace : “ANA QATILUL IBRATI,LA YAZKURINI MU’UMIN ILLAS TA’ABAR ma’ana Nine wanda aka kashe domin IBRA wato domin darasi -kayi adifa kayi kuka amma ka wuce nan ka dauki darasi kamar kissar Yusuf day an uwan shi a cikin Al-Kur’ani,duk Allah ya bada kissar ne saboda ISTI’IBAR wato ka wuce kissar ka dauki darasi ,to haka yake ga Husain (as),IBRA daga UBUR wato abin da ake wuce shi,ma’ana ana so ka wuce abin ka je bayan shi-Mu’umini (da kaidin imani) ba zai tuna ni ba face sai ya dauki darasi.Kullum a cikin daukan darussa ake dangane da Husain,ka da ku damu da zagi,wannan shine mafi karancin hakki da zaka iya ba Husain (as),shi yasa muke cewa YA LAITANA KUNNA MA’A KUM FA NAFUZA WALLAHI FAUZAN AZIMA.ILLAS TA’ABAR face cewa sai ya dauki darasi.Darassu muna ganin su koda yaushe a yau,darasin yau shine shubhohi da ake sanya wa a lullube abin da ya faru da Husain a ranar Ashura a Karbala wanda ba a wannan ranar shubhohin suka faru ba kad’an,har aka manta da falsafar tashin Husain (as) wato ya zama an sanya ka a cikin jidali da DIALECTIC wanda babu fa’ida ko SAMARA a cikin su sai don a gafalar da kai daga ainihin darasin.Daga cikin irin wannan shubhohin masu yawan gaske wadanda basu da iyaka,kun sani suna cewa wai Imam Husain ya fitone saboda neman duniya maslan,an kashe shi da takobin kakan shi.Kun sani akan cewa suna cewa Yan shi’ah su suka kashe Imam Husain,kun sani kun sani abubuwa masu yawa.Amma daga cikin shubhohin kun sani suna cewa ranar Ashura ba ranar bakin ciki bane kuma ba ranar farin ciki bane,wanda yake cewa ranar bakin ciki bane ba ranar farin ciki bane sunan shi Basalafe Bawahabiye Ba’umawiye saboda I’itiqadin Ibn Taimiyya ne kuma karantar wa shi ce,wanda suke ce ma Shaikhul Islam amma ba sa kayyade Islam din da Al-Umawiy wato kenan fitar dashi ko bambamce shi da Al-Muhammadiy Al-Asil.Sai nake cewa in ka samu kan ka a wani yanayi wanda ba bakin ciki kake kuma ba farin ciki kake ba to me kake yi ?Ka taba ganin irin wannan yanayin a dan Adam?Wato neutral level haka shi bai farin ciki sannan bai bakin ciki,mutum ne wannan ?Wato mutum ne wanda ya rasa Adifa din shi gabaki daya,wannan ba ita bace shubhar da nake so in yi magana akai ba,kawai ina ba da misali ne na irin abinda suke kawo domin su lullube maka abin da ya faru da Husain (as).288