15 Nuwamba 2015 - 19:31
Amurka da Rasha sun amince za su tattauna kan Syria

Shugaban Amurka Barack Obama da na Rasha Vladmir Putin sun amince da shirin zaman tattaunawar Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Syria cikin gaggawa, kamar yadda majiyar fadar white ke tabbatarwa.

Shugabanni biyu wadanda suka gana a taron G20 sun ce akwai bukatar tsagaita wuta da kuma yin kokarin mayar da kasar kan turbar siyasa.

Wannan dai ya kasance karon farko da Rasha da Amurka ke ganawa na tsawon mintoci 35, tun bayan lokacin da Rasha ta kaddamar da hari a Syria. 289