Kakakin rundunar sojin kasar, Sani Kukasheka Usman, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce soji sun kashe 'yan Boko Haram bakwai, a fafatar da suka kwashe sa'oi biyu suna yi.
Ya kara da cewa, dakarunsu sun kwato mota kirar Toyota guda daya, da bindigogi kirar AK-47 goma sha daya, da bindigar Shilka daya, da bindigar harbo jiragen sama guda daya da gurneti shida da alburusai da dama.
A cewar sa, dakarun sojojin sama na ci gaba da yin luguden wuta kan 'yan Boko haram din da ke yunkurin komawa dajin Sambisa da zummar murkushe su. 289