8 Nuwamba 2015 - 13:13
An cafke limamai bisa zargin ta'addanci a Senegal

Jami’an tsaro a kasar Senegal sun cafke wasu limaman addinin musulunci a birane da dama na kasar, bisa zargin yin alaka da kungiyoyi ta’addanci.

An dai kama limaman ne a garuruwan Kolda, Guediawaye, Khaolack da kuma Rufisque…. a daidai lokacin da kasar shirin daukar nauyin taron kasa da kasa kan samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya daga ranar litinin.

Senegal dai ta yi makotaka da kasashen Mali da Mauritaniya, wadanda ke fama da kungiyoyin masu tsatsauran ra’ayin kishin islama kamar Alqaida da kuma Mojao. 289