12 Oktoba 2015 - 16:51

Rundunar Sojin Rasha tace ta kai hare hare sau 63 kan mayakan ISIS dake Syria cikin sa’oi 24, a ci gaba da yunkurin ta na murkushe yan ta’addan dake kashe rayuka baji ba gani.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Igor Konashenkov yace an kai harin ne a Hama, Latakia, Idlib da Raqa kuma an lalata sansanin mayakan ISIS 53, cikin su harda cibiyar bada umurnin kungiyar da wuraren horar da mayaka 4 da sansanin aje makamai 7.

Wata majiya daga Gwamnatin Faransa na bayyana cewa jiragen yakin Faransa sunyi nasarar kashe wasu yan kasar Faransa dake marawa yan ta'addan Isil a Syria . 289