Wani shaidan gani da ido mai suna Ezz Zanoun ya ce , Jami’an tsaron na yawaita harbe harben bindiga akan iyakar, amma na yau ya wuce misali.
Cikin wadanda suka rasa rayukansu, akwai yaro mai shekaru 15 da Jamian suka bindige har lahira kuma akalla mutane 10 cikin mutane 70 da suka jikkata na cikin mawuyacin hali kamar yadda wata majiyar kiwon lafiya ta sanar.
A lokacin da ya ke gabatar da huDuba a yau jumma’a, shugaban Hamas, Isma’il Haniyeh ya yi kira ga al-ummar Falasdinawa da su kara kaimi wajen arangama da dakarun Isra’ila a yankin yamma da kogin Jordan da kuma gabashin birnin kudus.