Hukumomin sun ce an dauki matakin ne da nufin magance matsalar hare-haren kunar bakin-wake da ake fuskanta, musamman yadda akan yi amfani da wasu mata sanye da Hijabi.
Malamai a jihar sun ce sun gamsu da dokar bisa la'akari da yanayin dar-dar da ake ciki a fadin jihar.
Ko a baya ma gwamnatin jihar ta Diffa ta yi hani da sanya burka ga mata sakamakon karuwar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram a sassan jihar.
Jihar Diffa dai na daya daga cikin jihohin da 'yan kungiyar Boko Haram suka mayar karkatacciyar kuka a jamhuriyar Niger.288