Sanata Kabir Marafa daya daga cikin 'yan majalisar ta dattawa ya shaida wa BBC cewa wasu tsirarun mutane sun jirkita da sake wa kundin tsarin zauran fasali domin ya yi dai da muradinsu na kasancewa jagororin majalisar.
Ya ce kawo yanzu ba bu wanda ya san iya adadin sauye-sauyen da aka yi wa kundin har sai an yi cikakken bincike.
Wannan dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan majalisar ta dattawa suke komawa bakin aiki bayan kwashe makonni biyar suna hutawa.
A na dai sa ran cewa wannan batu shi ne zai mamaye zaman majalisar na yau, al'amarin da wasu ke ganin ka iya fama ciwon da ke damun zauren.
Tun dai bayan da tsohon gwamnan jihar Kwara da ke arewa maso tsakiyar kasar, Sanata Bukola Saraki da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu suka samu nasarar darewa kan kujerun shugaban majalisar da ta maitaimaka masa, rikici ya yi kamari a zauran.
Rundunar 'yan sandan kasar ta gudanar da bincike dangane da batun sauya kundin ta kuma nemi ofishin ministan shari'a da ya bayyana shin ko yin hakan ya saba wa dokokin kasa.288