16 Yuni 2015 - 15:59
An daure shaikh Salma shekara hudu

Shugaban jama’iyar al’wafag wanda yake tsare tun shekarar data wuce a yau ne aka yanke masa hukuncin daurin shekara hudu

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-shaikh Ali Salman shugaban jama’iyar musulunci ta al’wafag a hukuncin da wata kotun Bahrain ta yanke masa ayau ta daure shi shekara hudu a gidan yari.

Jama’iya al’wafag ta sanar da yanke hukuncin ne a shafinta na yada labarai inda ta tabbatar da yanke hukuncin.

Malami dan gwagwarmaya a kasar Bahrain an kama shi tun shekarar data wace ba tare da wani  dalili mai karfi ba.

Shaikh Salman dan shekara 50 ana tuhumar shi da laifin neman kawo canji da kuma ingiza mutane da kada su yarda da tsarin dokokin dan niya na hukumar kasar Bahrain.

Ali alsud, memba a jama’iyar al’wafaq yace, wannan hukuncin ba komi bane sai dai siyasa da kama karya.288