Shugabannin na Nijar da Faransa sun yi wannan kiran ne a ranar Talata, lokacin da shugaban na Nijar Muhammadu Isufu ya gana da takwaran nasa na Faransa a birnin Paris.
Muhammadu Isufu ya ce "Dole mu matsa musu lamba su sanya hannu ta yadda za mu samu a mayar da 'yan kishin Islama saniyar ware."
Kazalika shugabannin sun yi kira ga kasashen yankin sahel da su karfafa huldarsu domin dakile kungiyar Boko Haram.
A watan da ya gabata ne gwamnatin Mali da wasu kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya da kungiyoyin kasa da kasa suka sa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Amma manyan kungiyoyin 'yan tawayen kasar suka bujire wa yin hakan.ABNA