Bayanai sun ce wata mata 'yar kunar bakin wake ce ta tayar da bam din a lokacin da mutane ke hada-hada a cikin kasuwar.
Kawo yanzu babu bayanai a hukumance na adadin wadanda suka rasu.
Hakan na zuwa ne bayan da aka kwana cikin zullumi a Maiduguri sakamakon jin karar fashewar abubuwa da ake zargin Boko Haram ne suka harba.
A karshen makon da ya wuce, an hallaka mutane fiye da 30 a jihohin Yobe da Borno a wasu har-haren bam.
Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya ce shalkwatar tsaron kasar za ta koma Maiduguri domin murkushe ayyukan Boko Haram.ABNA