Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin shahidai a zirin Gaza ya karu zuwa 51,439.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya kawo rahotan cewa: Bisa ga wannan rahoton, tun daga ranar 18 ga Maris, 2025, inda wata Sabuwar guguwar harin ta'addancin Isra'ila ta ci gaba da yi kan Gaza, mutane 2,062 ne suka yi shahada a zirin Gaza, yayin da wasu 5,375 suka jikkata.
A gefe guda kuma rundunar Qassam sun ce: Mun bindige sojojin mamaya 4 da suka hada da sojoji biyu a gabashin Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza.
Your Comment