Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait (As) -Abna- ya habarto bisa nakaltowa daga Tashar talabijin ta Aljazeera inda ta watsa bidiyon zanga-zangar da aka gudanar a garuruwa daban-daban na kasashen Turai domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu a zirin Gaza.
Al'ummar Birtaniya sun gudanar da zanga-zanga a birnin Manchester domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu da Gaza.
Birtaniya, Faransa da Jamus sun yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a daren jiya Juma'a, gwamnatocin kasashen Jamus, Faransa da Birtaniyya sun yi kira da a gaggauta dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza tare da yin kira ga Isra'ila da ta ba da damar kai agajin jin kai a yankin da aka yi wa kawanya".
Your Comment