31 Mayu 2025 - 19:14
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kashe Kwamandan Hizbullah Sashen Makamai Masu Linzami

Sojojin Isra'ila sun sanar da kashe "Mohammad Ali Jamoul" kwamandan sashin makami mai linzami na Hizbullah a gundumar Al-Shaqif ta "Deir al-Zahrani", dake kudancin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: rahoton da tashar talabijin ta Channel 12 ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta fitar na nuni da cewa ta kashe "Muhammad Ali Jamoul" daya daga cikin kwamandojin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon.

Kakakin rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ya sanar da cewa sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kashe Muhammad Ali Jamoul tare da shahadantar a wani hari da wani jirgi mara matuki da aka kai kan motarsa a garin Deir al-Zahrani da ke kudancin kasar a safiyar yau.

Isra'ila Ta Kashe Kwamandan Hizbullah Sashen Makamai Masu Linzami

A halin da ake ciki kuma, majiyoyin na kasar Labanon sun rawaito cewa, Muhammad Ali Jamoul (mai shekaru 33) wanda shi ɗaya ne daga kwamandan sashin makami mai linzami na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ne yayi shahada a wani hari da jiragen sama mara matuki na mamaya suka kai a kan hanyar Deir al-Zahrani-Nabatiyya kusa da gadar masu tafiya a kafa a lokacin da yake tafiya masallaci a cikin motarsa ta kashin kansa domin yin sallar asubahi.

Kisan "Muhammad Ali Jamoul", kwamandan sashin makami mai linzami na Hezbollah, bayan wannan harin da Isra'ila ta kai da jirage marasa matuka.

A cewar wani rahoto da gidan talabijin na Channel 12 na Isra'ila ya bayar, kakakin sojojin Isra'ila ya yi ikirarin cewa Shahid Jamoul ya kai hare-haren ɓarin wuta da dama a kan 'yan mamaya da sojojin Isra'ila a lokacin yakin.

Har ila yau kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta tabbatar da shahadar "Muhammad Ali Jamoul" a hannun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a garin Deir al-Zahrani da ke kudancin kasar Labanon.

Wannan shi ne karo na farko da Isra'ila ta kai hari ga irin wannan zurfin yanki da ake daukarsa a matsayin keta iyaka a fili ga ikon Lebanon.

Jamul dai ya fito ne daga dangi ‘yan gwagwarmaya, kuma a baya dan’uwansa ya yi shahada a yakin Yahmar Shaqif a lokacin yakin kwanaki 66 (keta iyakar da Isra’ila ta yi kan Lebanon a baya-bayan nan).

Your Comment

You are replying to: .
captcha