30 Mayu 2025 - 21:52
Source: ABNA24
Hadafin Yin Aure A Musulunci Shine Kaiwa Ga Kusancin Ubangiji 

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Wanda ya yi hakuri da cutarwar matarsa, Allah zai ba shi ladan Annabi Ayuba, kuma macen da ta yi hakuri da cutarwar mijinta, Allah zai ba ta ladan Asiya, matar Fir'auna".

Takaitacciya Huɗubar Sallar Juma'a Ta Wannan Makon A Garin Aleeshahr, Ranar 30 ga Mayu 2025 daga bakin Liman Hujjatul Islam WalMuslimeen Hamidi Nejad limamin masallacin Birni.

Muna cikin watan Zul-Hijja, kwanakin farko na wannan wata sun zo daidai da kwanakin daura auren Amirul Muminin (AS) da Sayyida Fatima Zahra (AS) a wannan lokaci na so in kawo wasu abubuwa game da aure.

Na farko: Manufar aure a musulunci ya sha bamban da wanda ba na musulunci ba. A cikin auren wadanda ba Musulunci ba, manufar aure ita ce samun riba ta abin duniya, amma a Musulunci manufar ita ce samun riba ta ruhiyya. Don haka a cikin suratul Rum aya ta 31 cewa: “Allah ya sanya muku matan aure Gareka domin ku samu nutsuwa. Kuma a cikin suratun Ra’ad aya ta 38 cewa: “Da ambaton Allah zukata suke samun natsuwa”. Don haka aure wata kafa ce ta ambaton Allah. Ya zo a ruwaya cewa, lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam) ya tambayi Imam Ali (As) bayan aurensu shin ya ka samu matarka, sai ya ce: “Mafi alherin mai taimako wajen da’a ga Allah", wato wani mutum kamar Amirul Muminin (AS) shi ma ya zama tana ƙara samun daukakar daraja ta ruhi ta hanyar yin aure.

A ruwaya daga Ali (a.s) an ruwaito cewa wata rana ina cikin gida ina aiki. Manzon Allah (S.A.W) ya zo ya ce, “Ya Ali, duk wanda ya taimaki matarsa da aikin gida, bai yi baqin ciki da yin hakan ba, Allah zai ba shi ladan shahidai dubu kowane dare da rana, wannan lada Imam Ali (a.s) ba zai sameta ako ina ba, don haka manufar aure ita ce mu kai ga Allah da ruhiyya, idan muka yarda da haka, to ko matarmu ta kasance mai kyau ko marar kyau, hadafin yin aurennu ya samu nasara, kuma ranmu ba zai taba ɓaci don wai abokin aurenmu ya zamo ba mai halin kirki. kuma rabuwa ba zata taɓa faruwa ba har abada domin muna so mu kusanci Allah ta hanyar aure.

Idan har abokin aurenmu yana da halin kirki ta hanyar yi masa hidima idan kuma abokin aurenmu baya da halin kirki ta hanyar hakuri da abun da ya ke yi na cutarwa zamu isa ga hadafin da mu kai niyya.

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Wanda ya yi hakuri da cutarwar matarsa, Allah zai ba shi ladan Annabi Ayuba, kuma macen da ta yi hakuri da cutarwar mijinta, Allah zai ba ta ladan Asiya, matar Fir'auna". Ya kuma ce game da yi wa miji hidima, idan mace ta bawa mijinta ɗan gwagwado na ruwan sha, kaɗan hakan ya fi azumin yini da yin sallar dare tsawon shekara. Idan muka yi la’akari da wadannan ruwayoyin, ya kamata mu san girman daraja na miyagun mata. Mu sani cewa ta dalilinsu mun fi saurin zuwa aljanna fiye da matan kwarai. Muguwar mace takan ginawa kanta jahannama, amma ta kai mijinta zuwa aljanna.

Your Comment

You are replying to: .
captcha