31 Mayu 2025 - 22:14
Source: Quds
Yamen Ta Gargadi Kamfanonin Da Ke Aiki A Yankin Falasdinun Da Aka Mamaye Da Su Fice Cikin Gaggawa

Wani jami'in ma'aikatar tsaron Yemen ya sanar da cewa: Ma'aikatar tsaron Yemen ta gargadi bangarorin ketare da su fice daga kasar Falasdinu da aka mamaye

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti na kasa da kasa (ABNA) ya habarta cewa: Masu zuba jari na kasashen waje da kamfanonin da ke aiki a cikin Falasdinu da aka mamaye ya ya zama wajibi su fice da sauri, saboda yanayin dake tafe ba zai kasance na lafiya bag are su. Zai fi kyau su ci fice tun da sauran lokaci.

An kera makamanmu masu linzami ta yadda idan aka nufi abu to tabbas zai je gare shi, idan kuma aka tarwatsa su guntattkinsu zasu kai ga hadafin da ake so kuma su mayar da tsarin tsaron abokan gaba mara amfani.

Dole ne kowane maƙiyi ya yi taka tsantsan da makamanmu masu linzami da guntattakinsu. Makamai masu linzami na Yaman ba za su tsaya ba har sai an daina ta'addanci, an kuma dage wa jama'armu hari a Gaza.

Jami'in ma'aikatar tsaron kasar Yemen ya kuma jaddada wa 'yan sahayoniyawan cewa, manufofin Netanyahu na aikata laifuka za su tsawaita kwana da darare a wuraren mafaka a cikin kwanaki masu zuwa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha