14 Nuwamba 2024 - 20:04
Sayyid Hasan Nasrullah Bawan Allah Ne Da Samun Kamarsa A Yanzu Zai Yi Wuya

Wannan bayanin ya fito daga bakin wani mahalarci taron girmama shahidan gwagwarmaya da aka gudanar a Iran wanda taron ya samu halartar baki daga sassa da dama na duniya wanda kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bait As ABNA ya samu tattaunawa da su abinda ke biye wani tsakura ne tofa albarkacin baki da bakin wannan taron su kayi dangane da tafarkin gwagwarmaya da kuma shahidan da ake samu akan wannan tafarki mai tsarki.