1 Nuwamba 2024 - 18:13
Hamas: Sharuɗɗanmu Ba Ma Su Canzuwa Ba Ne.

Duk wata tattaunawa da aka gabatar mana da take biyan bukatun al’ummarmu da kuma kawo karshen radadin da suke ciki, to za mu bi ta ba tare da bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: Masu mamaye suna ba da ra'ayoyin tsari na wofi ne kawai, ba tsari na gaske ba, masu mamaye suna ba da ra'ayoyin da ke sa su zama kamar sune suka ci nasara.

Duk wata tattaunawa ko yarjejeniya dole ne ta kai ga ƙarshen tsagaita wuta duka ba wai wacce bada damar tsagaita wuta na wani ɗan lokaci na zaluncin gwamnatin Sahayoniya.