Yahudawan sahyoniya 20 ne suka samu raunuka sakamakon harin da jiragen yakin Hizbullah suka kai a sansanin na Golani.
Tashar Talabijin ta 12 ta gwamnatin sahyoniyawan ta sanar da cewa sojoji 20 ne suka jikkata sakamakon harin da jiragen yakin Hizbullah suka kai a sansanin sojojin na Golani sansanin da ke yankin Binyamina kusa da Haifa a arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye.
An bayyana cewa yanayin wasu daga cikin wadanda suka jikkata yana da tsanani.
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya nakalto majiyar soji na cewa wannan harin shi ne hari mafi muni tun farkon yakin wanda ake tunanin an nufi wani babban jami'in tsaron Isra'ila ne
Majiyoyin yaren yahudanci sun ruwaito harin roka da jirgin sama mara matuki da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai a yankunan arewacin Palastinu da aka mamaye da suka hada da Acre, Nahariya da Haifa.
Wadannan majiyoyin sun jaddada cewa an yi ta jin kararrawar gargadi a sassan arewacin Palastinu da aka mamaye da suka hada da Acre, Haifa, Al-Khadira, Nahariya da Ras al-Naqourah.
Majiyoyin Isra'ila sun kuma bayar da rahoton faruwar fashewar abubuwa a Haifa da Acre bayan wannan harin.
Wadannan majiyoyin sun jaddada cewa, wani jirgin mara matuki ya kuma kai hari a sansanin soji na tudun Golani da ke Acre.
Shima an ruwaito tabarbarewar yanayin wasu da suka samu raunuka sakamakon harin da jiragen yakin Hizbullah suka kai.
Kamfanin dillancin labaran Isra'ila ya bayar da rahoton cewa, adadin wadanda suka jikkata a harin da jiragen yakin Hizbullah suka kai ya kai mutane 28, wadanda wasunsu na cikin mawuyacin hali wanda kusan Anbulansa hamsin ne suka kai dauki zuwa gurin da aka kai harin
Jiragen sama masu saukar ungulu na Isra'ila da motocin daukar marasa lafiya sun isa wurin da kungiyar Hizbullah ta kai harin da jiragen yaki marasa matuka domin jigilar wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
Inda Channel 12 Ibrananci: Wani jirgin mara matuki ya kai hari a kudancin Haifa kuma rahotannin farko sun nuna cewa mutane da dama sun jikkata a wurin da hadarin ya afku.
Kafofin yada labaran Isra'ila sun kara tabbatar da cewa: Jirgin dai mara matuki ya nufi gidan sayar da kayan abinci na sansanin Golani da ke Acre kuma an samu munanan raunuka a wurin.
Wasu majiyoyin Falasdinawa sun bayar da rahoton tabarbarewar yanayin dakarun sojin Isra'ila 8 a harin da kungiyar Hizbullah ta kai.
Adadin wadanda suka jikkata a harin da kungiyar Hizbullah ta kai da jirage marasa matuka ya karu zuwa mutane 40
Kungiyar Red Star ta Daoud ta sanar a birnin Haifa cewa adadin wadanda suka jikkata a harin da jiragen yakin Hizbullah suka kai a sansanin na Golani ya karu zuwa 40.
Kimanin 10 daga cikin wadanda suka jikkata yanzu haka suna cikin mawuyacin hali.
Gidan rediyon sojojin yahudawan sahyoniya ya tabbatar da mutuwar sojoji 3 ya zuwa yanzu.
