2 Satumba 2024 - 14:59
'Yan Shi’a A Najeriya Sun Yi Muzahara Don Nuna Adawa Da Zaluncin Da Ake Yi Masu

Mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya sun yi zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin da 'yan sanda suka yi wa wasu 'yan mata da suka halarci taron Arbaeen din Imam Husaini As.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya habarto maku cewa: dubun dubatar mabiya Shi'a a Najeriya a yankuna daban-daban na kasar sun yi Allah wadai da matakin da jami'an 'yan sanda suka dauka na cire hijabi daga kan wasu 'yan mata da matan aure a yayin gudanar da tattakin Arbaeen din Imam Husaini As na shekara-shekara da aka saba gudanarwa wanda kuma wannan mummunan aikin babban take hakkin Allah ne da haƙƙin mutane 

Kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka wallafa, an gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a garuruwa daban-daban na kasar.

Muzaharar dai ta faru ne bayan da aka fitar da wani faifan bidiyo mai tsawon minti daya da dakika 21, inda jami’an ‘yan sanda ke cire hijabi daga kan wasu mata da suka halarci taron Arbaeen din Imam Husaini As.

Masu zanga-zangar a yayin da suke yin Allah wadai da wannan abin kunya, sun jaddada cewa, wannan mataki babban laifi ne, kuma cin fuska ne ga addinin musulunci ga 'yan kasar.

A cikin wata sanarwa da masu zanga-zangar suka wallafa, an bayyana cewa: abin da jami'an suka yi wa 'yan mata da matan auren cin zarafi ne na 'yancin addini da kuma saba wa kundin tsarin mulki da dokokin kasa da kasa. Har ila yau, sun jaddada cewa: za su kai kara ga kotun koli don magance wadannan take hakki na 'yan kasa, musamman mata musulmi.

Masu zanga-zangar sun yi nuni da cewa: “Hijabi” addininmu ne da al’adunmu da kuma hakkinmu, kuma aikata hakan cin mutunci da cin fuska ga musulmi da addinin Musulunci.

Sun kara da cewa: Jami'an 'yan sanda suna da cikakkiyar masaniya kan matsayin hijabi a tsakanin musulmi, amma sun yi hakan ne da gangan. Muna Allah wadai da wannan aiki, kuma muna kallonsa a matsayin cin mutunci ga Musulunci da Musulmi.