Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: an
gudanar da biki da shagulgulan girmama ‘yan jarida a taron shekara shekara na
abokan aikin kamfanin dillancin labaran Ahlul-baiti (a.s.) - ABNA - wanda ya
kasance a ranar Laraba 06 ga Agusta, 2024 tare da halartar Ayatullah Ridha
Ramizani, babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (a.s.) ta duniya a zauren
taron wannan majalissar da ke birnin Qum. A cikin wannan bikin, an buɗe tare da
baje kolin littafin Mai taken: samfurin Amintacciyar Rayuwa a cikin yaren
Swahili.
Hoto: Hadi Cheharghani















































