Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: an
gudanar da jana’izar shahid Fu’ad Shukri da ake yi wa lakabi da “Sayyid Mohsen”
babban kwamandan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon bayan jawabin
Hujjatul-Islam Wa Muslimin, "Sayyid Hasan Nasrallah", babban
sakataren wannan yunkuri, a kudancin yankin Dahiya, a birnin Beirut, babban
birnin kasar Lebanon. Wannan fitaccen kwamandan kungiyar Hizbullah ya yi
shahada ne a cikin 'yan kwanakin da suka gabata a wani hari ta sama da sojojin
yahudawan sahyoniyawan suka kai a wani gini da ke unguwar "Harah
Harik" a kudancin birnin Beirut.








































