Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa: Ɗalibai masu karatu a Jami'o'i daban-daban a birnin Tehran ne suka gabatar da taron cika shekaru goma da waki'ar Quds wanda Yan Uwa 33 tare da Ƴaƴan Jagora Sayyid Zakzaky (H) su uku su kayi Shahada (Shahid Ahmad, Shahid Hamid da Shahid Mahmud).
Taron ya gudana a cikin Haramin Imam Khumaini (Qs) wanda Ummu Zeenatuddin Ibraheem (Ummus-Shuhada) ta zama mai jawabi a wajen taron.
Da farko Ummu Zeenatuddin ta ziyarci Imam Khumaini (Qs) tare da yin addu'a a makwancinsa daga nan suka karasa wajen da ake taron na 25July.
QodsDay.
25July20114.
28/07/2024











