Kamfanin dillancin labaran shafin
sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: bayan
shahadar babban mujahid, Isma'il Haniyyah shugaban ofishin siyasa na kungiyar
Hamas, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike
da sakon ta'aziyya ga al'ummar musulmi, bangaren gwagwarmaya da kuma al'ummar
musulmi masu daukaka na Falasdinu dangane
da shahadar wannan jajirtaccen shugaba kuma fitaccen mujahid din Palastinu yana
mai jaddada cewa: Da wannan mataki ne gwamnatin sahyoniyawa mai aikata laifuka ta
'yan ta'adda ta shirya wa kanta saukar azabar sakayya mai tsanani, kuma muna
ganin ya zama wajibinmu mu daukai fansar jinin wanda ya yi shahada a cikin
kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Da wannan munsabar ne kafar yada labarai ta
KHAMENEI.IR ta fitar da hotunan ganawar da wannan shahidi na Falasdinu wanda ya
yi da jagoran juyin juya halin Musulunci.

















