20 Yuli 2024 - 19:34
Bidiyo Cikakkun Bayanai Na Harin Da Gwamnatin Yahudawa 'Yan Mamaya Ta Kai A Yaman

Yamen Zata Mayar Da Martani: Tashar Jiragen Ruwan Haifa Da Aka Mamaye Ita Ce Hadafin Da Yamen Za Ta Kai Wa Hari.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin yada labarai na kasar Yaman sun rawaito cewa, awowi da su ka gabata sojojin gwamnatin Yahudawa da ke mamaya sun kai hare-hare ta sama sau 10 a yankuna 2 na tashar wutar lantarki ta yankin Salaf da tankunan mai a tashar jiragen ruwa na Hudaidah.

Tashar yada labaran Isra'ila: 'Yan Italiya sun taimaka mana da wani jirgin sama mai dakon mai a sararin samaniyar Yaman.

Muhammad Al-Bakhaiti, memba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullah: Gwamnatin Sahayoniya za ta biya bashi mai tsada kan harin da ta kai kan fararen hula, kuma za mu mayar da martani ga tsanani da tsanantawa.

Majiyar Yaman: Tashar Jiragen Ruwan Haifa Da Aka Mamaye Ita Yamen Hadafin Da Za Ta Kai Wa Hari.