18 Yuli 2024 - 10:49
Tasu'ah Da Ashura Tsakanin (Farinciki Ko Bakinciki)

lallai maƙiya Ahlul Baiti daga mutanen Sham (Siriya) sun kishiyanci abinda ƴan Shi'a ke yi (na baƙin ciki a ranar Ashura ), sun kasance suna yin girke-girke, suyi wanka, su sanya turare, su saka kayansu na alfarma, su ɗauki ranar a matsayin Idi da abinci iri-iri, suyi ta bayyana murna da farin ciki, ba komai yasa suke yin haka ba sai dan ƙiyayayya da kishiyantar yan Shi'a. Haka Ibnu Kathiir ya fada. A taƙaice dai yana magana akan cika ciki da aka fi sani a kasar Hausa.

Irin muguwar aika-aikan da da Banu Umayya suka yi a ranar Ashura kan zuriyar Annabi (saww) , basu da wata mafita ta ɓoye wannan mugun abu sai ƙirƙiro tatsuniyayoyi da ƙissoshin da basu da asali ad dangantasu ga Annabin Rahama (s).

Kamar mutum ne yayi kisan da baya so a gano shi yayi saboda hakan barazana ce babba gareshi - tun ballantana ace wanda ya kashe wani mutum ne mai daraja da ƙima - to duk yadda zai yi sai yayi wajen suturce wannan aikin nashi , ko da hakan zai sa ya bada duk abinda ya mallaka fansar aikinsa , ballantana kamar Banu Umayyah da suke da dukiya , mulki , kurkuku da malaman fada me kake tunanin ba zasu shirya ba, wajen ɓoye abunda sukayi yiwa Imam Hussain da iyalansa da Sahabbansa managarta a karbala ranar Ashura?

Kar kuyi mamaki dan sun ƙirkiro karairayi da labarai na banza da ke nuna falala da girman Ranar, inda suka ce ranar Ashura rana ce ta yalwatawa iyali , rana ce ta farin ciki, ana so ayi azumi, Sallah, sadaka, shafa kan maraya, sada zumunci, ziyarar malamai da sanya kwalli da sauransu. Babu shakka waɗannan abubuwa ne masu kyau a kan kansu cikin Addinin Musulunci, amma me yasa ba'a rawaito ƙarfafa yinsu ba sai a ranar da aka kashe jikan Manzon Allah (saww)? Ranar da akayi mummunan ta'addancin da ba'a taɓa irinsa ba a tarihin ɗan Adam akan iyalan Annabi Muhammadu (s)! Alal aƙalla ko ba'a yi baƙin ciki da juyayi ba to ai ba'a ce ayi farin ciki ko a yalwatawa iyali ba. Uwa uba yin murna da farin ciki da yalwatawa iyali (cika ciki ), mummunar bidi'a ce da Nasibawa (maƙiya Ahlul Baiti ) suka kirkirota dan su kishiyanci Musulmi ƴan Shi'a kan juyayi da alhinin da suke yi a ranar, da shedar manyan Malaman Ahlussunna Wal jama'a suka faɗi haka, Misali babban Malaminsu Ibnu Kasir a cikin Littafin (Albidaya WanNihaya , juzu'i na 8 , shafi na 220) yana cewa :

وقد عاكس الرافضة والشيعة يوم عاشوراء النواصب من أهل الشام، فكانوا إلى يوم عاشوراء يطبخون الحبوب ويغتسلون ويتطيبون ويلبسون أفخر ثيابهم ويتخذون ذلك اليوم عيدا يصنعون فيه أنواع الأطعمة، ويظهرون السرور والفرح، يريدون بذلك عناد الروافض ومعاكستهم.

Ma'ana: lallai maƙiya Ahlul Baiti daga mutanen Sham (Siriya) sun kishiyanci abinda ƴan Shi'a ke yi (na baƙin ciki a ranar Ashura ), sun kasance suna yin girke-girke, suyi wanka, su sanya turare, su saka kayansu na alfarma, su ɗauki ranar a matsayin Idi da abinci iri-iri, suyi ta bayyana murna da farin ciki, ba komai yasa suke yin haka ba sai dan ƙiyayayya da kishiyantar yan Shi'a. Haka Ibnu Kathiir ya fada. A taƙaice dai yana magana akan cika ciki da aka fi sani a kasar Hausa.

To haka su kansu sauran abubuwan da aka ƙirƙiro hadisai na abubuwan da akeso ayi a Ranar, kamar Azumi da Sallah da sauransu da muka ambata a baya, abubuwa ne da dalili da hujjoji suka tabbatar da ƙirƙirarsu da maƙiya Ahlul Baiti (a.s.) suka yi, dan kawai a rufe abinda ya faru a wannan ranar na aika-aika kan ƴaƴan Annabi (saww). Kai kace Annabi (s) bai yi kuka da baƙin ciki da abinda zai faru a ranar ba tun kafin ya faru, to ina ga ace Annabi (s) yana nan akayi wannan abu mai kake tunanin zai yi? To amma an ce karkayi juyayi da bakin ciki saboda da wanda aka kashe da wanda yayi kisan sun koma ga Allah, to shi Azumin da aka ce ayi saboda Annabi ya ga Yahudawa suna yi da yazo Madina, (wai dan murnar tseratar da Annabi Musa da hallakar da Fir'auna), shin Annabi Musa da Fir'auna basu koma ga Allah yayi hukunci akansu bane ko me? Watau kar kayi kuka da baƙin cikin abinda aka yiwa zuriyar Annabi (s) Amma kayi farin cikin hallakar da mutanen Fir'auna! Wannan wane irin Addini da tunani ne?

Tare da yazo cewa; Annabi yazo ya tarar da wai Yahudawan Madina suna yin wannan Azumi, da ya tambaya aka faɗa masa dalilinsu na yin hakan sai yace; Ai mu muka fi yahudawa cancanta da Annabi Musa idan shekara ta zagayo zan Azumci Ashura, shekarar da bata zagayo ba yayi wafati. To abun tambaya anan shine dama Manzon Allah (saww) shekara ɗaya yayi a garin Madina ba Goma ba? Lallai wannan magana akwai kwamacala da kwamɓale a cikinta.

Tare da haka duk shekara zaka ga wasu da ake kira manyan Malamai, suna shiga kafafen sadarwa na zamani suna yaɗa wadannan falalolin bogi da karya game da wannan Rana, tabbas hakan cutar da Annabi da iyalan gidansa ne sun sani ko basu sani ba wallahi, babu ta yadda za'a yi irin wannan aika-aika ga zuriyar Annabi sannan wani yazo yana faɗa maka ranar yalwatawa iyali ce! In kana da hankali da tunani ba zaka ko saurare shi ba, Tabbas Banu Umayyah da waɗanda suka kawo su sun cutar da Annabi (s) da madafan ikonsu, kurkuku, dukiya, da alkaluman miyagun Malaman fadar da suke sarrafa ƙwaƙwalen jahilai da wawayen mutane.

Allah ka sakawa Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka kan wannan mummunan zalunci da ta'addancin da ba'a gushe ba ana yi musu shi har a yau .

Wanda Ya Rabuta: Khadimul Ashrãf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


https://t.me/tafarkintsiratv