...Yau Mun Kawo Maku
Zikra Na Tarihin Yadda Manzon Rahama Yayi Kuka Dangane Da Abunda Za Samu Imam
Husain As A Ranar Ashura...
Allah Ta’ala ya bayar da labarin shahadar Imam Husaini (AS) ga mala'ikunsa da annabawansa shekaru aru-aru kafin Ashura. Hasali ma Allah Ta’ala da Mala’ika Jibrilu sune wadanda suka fara anbaton da juyayin wannan musiba ta shahadar Imam Husain As.
A cikin tafsirin suratu Baqara aya ta 27:
(و علَّمَ آدَمَ الأَسمَاء كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى الْمَلاَئِكَةِ فَقَالَ أَنبِئُونِي باسمَاء هَؤُلاء إِن كُنتُمْ صَادقین)
(Ya sanarda Adamu dukkan sunaye, sannan sai ya bijirar da su ga mala'iku sai ya ce ku bani labarin wadanan sunaye idan kun kasnace masu masu gaskatawa), malamai sun ce wannan koyarwar sunaye ita ce abin da Jibrilu ya karantar da Adamu inda ya ce masa;
"یا حمیدُ بحق محمد، یا عالي بحق علي، یا فاطرُ بحق فاطمة، یا محسنُ بحق الحسن و یا قدیمَ الإحسان بحق الحسین"
"Ya Hamidu bihaqqi Muhammad, ya Aaliyu bihaqqi Aliyu, ya Fadiru bihaqqi Fatimah, ya Muhsinu bihaqqil Hasan, ya Qadimul Ihsan bihaqqil Husain". Sai shi kuma Adamu ya maimaita hakan; Amma da ya ambaci sunan Husain, zuciyarsa ta raunana, hawayensa suka zubo. Sai ya ce: "Ya dan uwana Jibrilu! Me ya sa zuciyata ke karaya, hawaye na ke zubowa idan na anbaci mutum na biyar?" Jibrilu ya amsa da cewa: "Wannan Dan naka zai ga wani bala'i idan aka kwatanta shi da sauran bala'o'I to ‘yan kadan ne".
Kamar yadda dai irin wannan labari an kawo labarin shahadar Imam Husaini (a.s) dangane da Sayyidi Nuhu da Ibrahim da Musa da Zakariyya da kuma Annabi Isa. Amma mafi daci da raddai a cikinsu shi ne sanar da Annabin da wanda Imami ya kasance hantarsa ne kuma tsokar jikinsa kuma badadin ruhinsa:
Watarana Annabi (SAW) yana tare da matarsa Ummu Salma (R.a) sai Mala’ika Jibrilu ya sauka. Sai Annabi ya shiga daga ciki ya ce mata: "Kada ki bar kowa ya shigo". Bayan dan lokaci kadan sai Imam Husaini (a.s.) ya zo ya ce yana son shiga wurin Annabi. Ummu salma ta dauke shi ta rungume shi. Imam Hussain (a.s) yanata kuka sai Ummu Salamah ta yi masa magana mai dadi don ta kwantar masa da hankali; Amma kukan Imam Hussaini (a.s) ya tsananta. Har sai da Ummu Salama ta sake shi har ya shiga dakin ya zauna akan cinyar Annabi. Ganin haka sai Jibrilu ya ce wa Sayyidina Muhammad: "Al’ummarka za su kashe wannan dan naka".
A wani hadisin kuma, Sheikh Sadouq ya ruwaito daga Imam Bakir (a.s.) da isnadinsa, wanda zai iya zama ci gaban hadisin da ya gabata: Ummu Salama ta zo wajen Annabi, ta ga Husaini yana zaune a kan kirjin Manzon Allah (SAWA) Annabi yana kuka alokacin kuma akwai wani abu a rike a hannunsa da yake sumbatarsa.
Sai Manzon Allah (saww) da ya ga Ummu Salama ya ce: “Ya Ummu Salama! Wannan Jibrilu ne yake ba ni labari cewa za a kashe wannan yaron, kuma wannan kasar ce da za a kashe shi akanta, ki kiyaye ta a wajenki, duk lokacin da ta canja ta koma jini, to an kashe masoyina".
Ummu Salma ta ce: "Ya Manzon Allah! Ka roki Allah ya kawar maka wannan musibar".
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Na aikata haka, amma wahayi ya zo mini daga Allah cewa shi wata daraja ce da babu wani daga cikin halittu da zai kai gareta, kuma shi ne abin bi da ya ke yin ceto, kuma cetonsu karbabbe ne, kuma lalle “Mahdi” yana daga cikin ‘ya’yansa, don haka sun ji dadinsu wadanda suka kasance daga cikin masoyan Husaini, na rantse da Allah ‘yan Shi’arsa su ne masu ceto ranar kiyama.
Abdullahi bn Abbas yana cewa:
Na kasance ina kwance a gidana (a Madina) sai kwatsam sai muka ji wata kara daga gidan Ummu Salma, matar Manzon Allah (saww). Mutanen Madina maza da mata suka tafi zuwa gidanta.
Ni ma na je gidanta, da na isa wurin na ce: “Ya Ummul Mu’uminina, me ya sa kike kuka da raki? Ummu Salama ta waiwayo zuwa ga matan Hashimawa, ta ce: “Ya ku ‘ya’yan Abdulmuddalib, ku yi ta kuka tare da ni... na rantse da Allah, An kasha Husain shugaban samarin sama, masoyin Annabi".
Suka ce: "Ya aka yi kika sani?" ta ce: "Yanzu na ga Annabi a mafarki alhalin yana cikin kura da firgici cikin kura a kansa da fuskarsa, sai na tambayi dalili, sai ya ce: An kashe dana Husaini da iyalansa, kuma ni na binne su".
Na farka, sai na dubi turban kasar Husaini, wanda Jibrilu ya zo da shi daga Karbala, wanda na ajiye a cikin kwalba. Na ga wanna kasar ta koma sabon jini kuma yana tafasa a cikin wannan kwalbar...
Mu ma Muna yi ma ka ta'aziyya, ya Manzon Allah; “Ya Manzon Allah! Allah ya baka lada dangane da bala'in da ya samu Badadinka Husain da iyalansa"...
»یا رسول الله! آجَرَكَ الله في مصیبةِ ریحانتِكَ وسبطِكَ الحسین ... «
ــــــــــــ
✓ Madogara:
1. Al-Tabarani; Al-Mu'jam al-Kabir; juzu'i na takwas; Shafi na 285.
2. Sheikh Sadouq, Amali; Shafi na 120.
3. Sheikh Tusi; Amali; Shafi na 314.