Musulman Shi'a na Najeriya a garuruwan Abuja, Bauchi da Kano Katsina Zaria da Jos sauran manyan birane manya da kananan a Najeriya sun fara gudanar da taruka na Makokin muharram in da suke sanye bakaken tufafai tun ranar farko ga watan Muharram tare da halartar zaman makokin Imam Hussaini (a.s) wanda ya hada da gabatar da jawabai na abubuwan da suka faru a watan muharram da wake-wake da bugun kirji.
Ana ci gaba da zaman makokin Imam Hussain (AS) na tsawon kwanaki 10 a Najeriya; Har ila yau, taron Ashura na ranar goma ga watan Muharram a Najeriya ya hada da kafa dogayen jerin gwano a kan tituna, kuma mahalarta taron juyayin shahadar Imam Hussain (amincin Allah ya tabbata a gare shi) da sahabbansa suna gudanar da tarukan yayin da suke ta bugun kirzansu da rera wakokin juyayi.
