19 Yuni 2024 - 08:12
Dakarun Hizbullah Ta Kasar Labanon Ta Kai Hari Kan Wata Masana'antar Kera Makamai Ta Sahyoniyawa

Hizbullah ta kai harin kan wata masana'antar kera makaman Isra'ila a arewacin Falasdinu da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlal-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa: kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da kaddamar da wani sabon farmaki kan makiya yahudawan sahyoniya.

Dangane da wanna harin kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa mayakan mu sun yi nasarar kai hari kan masana'antar Balasan da ake kera makaman yahudawan sahyoniya da ke a Kibbutz Sasa da makamai masu linzami na Flaq.

A wani farmakin kuma kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hari kan shalkwatar bataliyar soji ta 411 ta gwamnatin sahyoniyawan a yankin "Naveh Ziv" da kuma wurin da sojojin yahudawan sahyoniya suke a wannan yanki a wani hari da jirgin sama mara matuki.

A gefe guda kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa ta kai hari kan wata tankar yaki ta Merkavar Isra'ila da ke sansanin "Hadab Yarin" da ke arewacin Palastinu da aka mamaya da wani jirgin kunar bakin wake tare da jikkata wasu 'yan mamaya.

Ta hanyar buga wannan hoton bidiyon da jiragenta mara matuki suka dauka, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta dauki hotuna da bidiyo daga dukkan wurare masu muhimmanci da tankunan sinadarai da mai da tashar jiragen ruwa na Haifa da ke arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, wanda ke suna daya daga cikin wuraren da ake son kaiwa hari a nan gaba a jiya Talata.

A cikin wannan faifan bidiyo, jirgin sama mara matuki na Hizbullah da aka fi sani da "Al-Hoodh" yana sintiri a tashar ruwan Haifa da aka mamaye ba tare da an kai masa hari ba tare da watsa hotuna masu inganci na aikin da aka ba shi.

Tun daga lokacin da guguwar Al-Aqsa ta fara kai hare-hare a ranar 7 ga watan Oktoba (15 ga watan Mehr) zuwa yanzu kungiyar Hizbullah da wasu kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a kudancin kasar Labanon suka kai farmaki kan wuraren da dakarun mamaya da kuma matsugunan yahudawan sahyoniya suke a arewacin Palastinu da suka mamaye.

Manufar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a cikin wannan farmakin ita ce shigar da wani babban bangare na sojojin yahudawan sahyuniya a arewacin kasar Falasdinu cikin yaki da kuma rage matsin lambar da ake fuskanta a zirin Gaza.

...................................

Ƙarshen Labarin / 268