8 Yuni 2024 - 16:33
Karin Wasu Bidiyoyin Na Kisan Kiyashin Da Sahayoniya Su Kai A Sansanin Nusairat

Gwamnatin yahudawan sahyuniya sun rusa tsakiyar Gaza da bama-bama, ta hanyar da gwamman jiragen yakin Isra'ila da jirage masu saukar ungulu su yi ruwan bama-bamai a tsakiyar zirin Gaza. Ya zuwa yanzu dai mutane 150 ne suka yi shahada, wasu da dama kuma sun samu munanan raunuka, kuma wadanda ba a san adadinsu ba suna karkashin baraguzan ginin.