
Bidiyoyin Yadda Yahudawan Sahyuniyawa Suka Shiga Masallacin Al-Aqsa Don Gudanar Da Ibadar Talmud A Safiyar Yau
5 Yuni 2024 - 06:50
News ID: 1463429
Tun da sanyin safiya zuwa yau ne sama da 'yan sahayoniya 500 'yan mamaya ne suka kai dafifin shiga masallacin Al-Aqsa karkashin taimakon jami'an 'yan sanda tare da gudanar da ayyukan ibada na Talmud. A halin da ake ciki dai wasu da dama daga cikin yahudawan sahyuniya sun yi ta rawa, da tattakawa, da kuma rera wakoki na tsokana, kafin su danna cikin masallacin Al-Aqsa da ke tsohon yankin Kudus. Wanda Sahayoniyawan sun yi wannan shirin ne don tsokana a birnin Quds a yau.
