Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ya habarta
cewa, an gudanar da taron tunawa da shahidan hidima da majalisar Ahlul-baiti
(A.S) da jami'ar Al-Mustafa Al-Alamiya suka gudanar a yammacin jiya Alhamis 30
ga watan 05 2024 – a dakin taro na Quds na Masallacin Imam Khumaini (RA) dake
birnin Qum. Manyan malamai wadanda suka gabatar da jawabi a wannan taron sun
hada da Ayatullah Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (a.s) ta duniya
da Hujjatul Islam Wal Muslimeen, Dr. Abbasi, shugaban Jama'atul-Mustafa da Hujjatul-Islam
Wal Muslimeen, Abdallah Al Daqqaq, shugaban makarantar hauza na Bahrain mazauna
birnin Qum.
Hoto: Hamid Abedi






































