11 Mayu 2024 - 14:52
Ayatullah Ramezani: Sanin Wilaya Da Mazhabar Ahlul Baiti (AS) Shi Ne Mafi Girman Ni'ima.

Fitaccen malamin Shi'a kuma jigo a Majalisar Koli ta Musulunci ta kasar Mali ya gana tare da tattaunawa da babban sakataren Majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya a yammacin yau.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Hujjatul-Islam Walmuslimeen, "Sayyid Muhammad Shawala Haidara" fitaccen malamin shi'a kuma jigo a majalisar koli ta Musulunci ta kasar Mali, a wata ziyarar aiki da ya kai kasar Iran birnin Qum, kafin azahar yau - Asabar 11 ga Mayu, 2024 ya gana tare da babban sakataren majalisar Ahlul-Baiti (a.s) inda suka tattauna.

Ayatullah “Reza Ramezani” bayan sauraron bayanan Hujjatul-Islam Walmuslimeen Shawala Haidara ya cewa: Allah ya haskaka zuciyarka da hasken Wilaya a matsayin daya daga cikin masu shelar Musulunci da mazhabar Shi’a.

Inda kuma ya yi masu jawabi yana mai cewa: Kai ya kamata ka taka rawar matsayin Sayyidina Jafar bin Abi Talib a cikin kasarku. Ya zo a cikin littafan tarihi cewa, lokacin da sarkin Habasha ya tambayi Jafar bin Abi Talib, wane ayoyi ne aka ambata game da Annabi Isa da Maryama a cikin littafinka? Ya karanta ayoyin suratul Maryam sai ga hawaye na zubowa daga idon Sarkin Habasha. Haka nan zaku yi kuma ku sanya hawayen farin ciki na zubowa daga idanuwan Kiristoci ta hanyar karanta ayoyin Alqur'ani.

Malamin manyan majami'u na Hauza ya ce sanin wilaya da mazhabar Ahlul Baiti (AS) shi ne mafi girman ni'ima. Ni'imar Mazahabar Ahlul Bayt A's ba Abar gwamawa ce dukkan dukiyar duniya ba. Wani daga cikin talakawan ‘yan Shi’a ya zo wajen Imam Sadik (AS), ya koka da talaucinsa, ya nemi taimako. Sai Imam (As) yayi ta fadin cewa kai ba fakiri ba ne, ya kara da cewa: Idan wani daga mawadata ya ce, zan cika maka kasa da azurfa, kuma ina rokonka da ka cire soyayya da waliyyar Ahlul-baitin Annabi daga zuciyarka kuma ka sami yin abuta da soyayya ga makiyansu, shin za ka yarda ka yi hakan? Sai ya ce: A’a dan Manzon Allah (SAW) ko da ya cika duniya da zinare! Imam ya ce, to kai ba talaka ba ne, talaka shi ne wanda ba shi da abin da kake da shi.

Ya nanata cewa: Yana da kyau a isar da koyarwar Ahlul Baiti (AS) ta hanyar da ta dace, wato a sassanta na daidaiku da na zamantakewa da na Ruhiyya da na siyasa ga masu sauraro. A tafiyata ta Gabashin Afirka na ce ku kun fito ne daga kabilar Bilalul Habasha ne. Bilal ya dauki maganar Annabi (SAW) a matsayin mu’ujiza, bai nemi wata mu’ujiza daga gare shi ba, kuma ya karbi Musulunci ba tare da wata mu’ujiza ba. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cewa a cikin al’ummar da ake bautar da bakar fata: “Babu bambanci tsakanin Balarabe da wanda ba Balarabe ba, ko tsakanin baki da fari sai da takawa. Mushrikai sun azabtar da Bilal da yawa, suka dora dutse mai nauyi a cikinsa don ya ci mutumci da zagin Annabi (SAW) ko ya dawo daga Musulunci, amma ya yi ta maimaita zikirin Ahad yana cewa: Ba zan koma shirka da bautar gunki ba.

Ayatullah Ramezani ya bayyana ka’idoji na Asasi guda biyu na Ahlul Baiti (a.s) cewa: Ahlul Baiti (a.s.) suna da ka’idoji guda biyu na tushe wadanda suke kore zalunci a Musulunci; Wato kada mutum yayi zalunci kuma kada ya bari a zalunce shi. Haka nan wasiyyar sayyidina Ali (a.s) da ya ce: "Ka kasance mai fada da azzalumi, kuma mai taimakon wanda aka zalunta." 

«كُونَا لِلظَّالِمِ خَصْماً وَ لِلْمَظْلُومِ عَوْناً»

Don haka bada kariyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga Palastinu da Hamas da kuma al'ummar Gaza da ake zalunta yana kan wannan al'amari ne, kuma Iran tana kare mutanen duniya da ake zalunta a matsayin tsarin ka'ida ta Shi'a da Ahlul Baiti (AS). A yau don tinkarar zalunci da kisan kare dangi na gwamnatin Sahayoniya, hatta muryar al'ummar Amurka da daliban Amurka sun taso, kuma hakan na nuni da cewa lamirin dan Adam a farke yake.

Ya ce game da yanayin koyarwar Ahlul Baiti (a.s.) cewa: koyarwar Ahlul Baiti (a.s) ta dace da lamirin dan Adam, don haka yake samun amsuwa a duniya kuma duniya tana yarda da shi.

Daga karshe babban sakataren majalisar Ahlul Baiti (A.S) ya yi nasiha ga Hujjatul-Islam Walmuslimeen Shawala Haidara yana mai cewa: Ku yawaita karatun Alkur’ani da Nahjul Balagha da Sahifa Sajjadiyah, domin kuwa waɗannan kafofin za su arzuta ku ta yadda za ku iya yin magana da tattaunawa tare da masana kimiyya da masu tunani da cikakken karfi.