7 Faburairu 2024 - 06:17
'Yan Sandan Amurka Sun Cafke Yahudawa Da Dama Da Ke Goyon Bayan Falasdinu

'Yan sandan Amurka sun kama wasu da dama daga cikin 'yan kungiyar Yahudawa masu goyon bayan Falasdinu a wannan kasa.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA- ya nakalto daga Kamfanin dillancin labaran Qud bisa nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera cewa: jami’an tsaro a jihar Pennsylvania sun kame sama da mutane 100 na wata kungiyar gwagwarmayar Yahudawa a Amurka.

Rundunar ‘yan sandan Amurka ta sanar da dalilin kame wadannan mutane, zanga-zangar da ‘ya’yan kungiyar suka yi a cikin ginin majalisar dokokin kasar da kuma goyon bayan Falasdinu.

Masu zanga-zangar dai sun so ne su sanyawa gwamnatin Sahayoniya takunkumi tare da daina saka hannun jari a kamfanonin Isra'ila don tallafawa Falasdinu.