13 Maris 2025 - 04:02
Source: ABNA24
Jagora: Ikirarin Da Amurka Ke Yi Na Son Yin Tattaunawa, Yaudarar Jama'a Ne Kawai.

Imam Khamenei A Ganawarsa Da Gungun Daliban Jami'a: Idan Amurka Da Mataimakanta Suka Yi Wauta, Martaninmu Zai Zamo Tabbatacce Ba Makawa.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya gana da gungun daliban jami'a da masu fafutuka daga sassan kasar. Jagoran ya ci gaba da cewa, sanarwar da shugaban kasar Amurka ya yi na shirin tattaunawa da Iran ba komai ba ne illa yaudarar ra'ayin jama'a, kuma yin tattaunawa da wannan gwamnatin ba zai dage takunkumin da aka kakaba wa Iran ba, sai dai zai kara dagula su da karin matsin lamba. Jagoran ya jaddada cewa, babu makawa Iran za ta mayar da martani da kai hari idan har Amurka da kawayenta suka kai wa Iran hari.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (ABNA) n kasa da kasa ya habarta cewa, a yammacin jiya Laraba 12 ga watan Maris din shekarar 2025 ne jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khamenei ya gana da dubban daliban jami’o’in kasar da kuma masu fafutuka a fagen siyasa, zamantakewa da al’adu da kungiyoyin jihadi na dalibai.

A farkon taron, jagora ya ba da shawarwari masu mahimmanci dangane da wasu koke-koke da batutuwa da kuma karfafa matsayin dalibai. Daga nan sai ya tabo abubuwa daban-daban guda biyu da matasan Iran suka samu wajen tunkarar kasashen yammacin duniya, inda ya ce: Kwarewa ta farko ta kai ga cin kashin kai, yayin da kwarewa ta biyu, wadda yunkurin dalibai na yanzu ke bi, ta ta'allaka ne kan koyon hakikanin kasashen yamma, da kokarin neman 'yancin kai, da kuma kaucewa matsalolin wayewar kasashen yamma.

Imam Khamenei ya ci gaba da gabatar da jawabinsa a kan batun tattaunawa da Amurka yayin da yake ishara da maganganun da shugaban kasar Amurka ya yi dangane da aniyarsa ta yin tattaunawa da cimma matsaya, da kuma aikewa da sako ga Iran, Jagoran ya bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na batarwa ga ra'ayin al'ummar duniya. Ya kara da cewa, "Ban samu wannan sakon ba, amma Amurka na kokarin yada wannan karyar na cewa Iran ba ta yarda da tattaunawa da fahimtar juna ba, yayin da wanda yake wadannan kalamai shi ne ya yaga sakamakon tattaunawar da muka yi da Amurka. "Ta yaya za mu sake yin tattaunawa da shi alhali mun san cewa ba zai bi sakamakon da aka samu ba?!”.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da wata makala da aka buga a cikin jaridun kasar inda aka rubuta aciki cewa: “bai kamata a ce rashin amincewar bangarorin biyu da ke yaki da juna ba ne zai hana zama a tattauna da kaiwa ga mafuta ba”. yana mai cewa: " Wannan ba daidai ba ne, domin idan bangarorin da ke tattaunawa ba su aminta da amincewar juna kan riko da sakamakon tattaunawar ba, zai zama tattaunawar a wanna yanayi shirme ne mara anfani”.

Jagoran ya ci gaba da cewa, "Tun da farko manufarmu a tattaunawar ita ce a dage takunkumin, kuma sai mukai sa'a, sannu a hankali tasirin takunkumin yana raguwa a kan lokaci".

Imam Khamenei ya kara da cewa, “Wasu Amurkawa kuma suna ganin cewa tsawaita wa’adin dokar zai rage tasirinsa; Bugu da kari, kasar da aka sanya wa takunkumin za ta samo hanyoyin da za ta bi domin lalata shi, mun kuma samo hanyoyi daban-daban don yin hakan".

Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga kalaman Amurkawa na cewa: Ba za mu bar Iran ta samu makamin nukiliya ba, yana mai cewa: Idan muna son kera makamin nukiliya, to Amurka ba za ta iya hana mu ba; Dalilin da ya sa ba mu da makamin nukiliya kuma ba ma nemansa shi ne, saboda wasu dalilai da aka ambata, ba ma bukatar irin wannan makamin”.

A wani batu kuma, Jagoran ya yi la'akari da barazanar da Amurka ke yi na kai harin soji a matsayin rashin hankali, yana mai jaddada cewa: Barazanar kai hari da kaddamar da yaki ba ya nufin cewa hare-haren za su kasance na bangare daya kadai ba ne, Ita ma Iran tana da karfin kariya daga harin da kuma mayar da martani, kuma ba makawa za tai hakan.

Imam Khamenei ya kara da cewa: Idan Amurkawa da mataimakansu suka aikata wani wautar soja kan Iran, to su ne za su fi shan wahala. Yaƙi ba abu ne mai kyau ba, kuma ba ma nemansa; Amma idan wani ya yi haka, martaninmu zai zama tabbatacce ba makawa”.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa, Amurka na fuskantar rauni, inda ya kara da cewa: A fannin tattalin arziki, manufofin siyasar ketare, siyasar cikin gida, al'amuran zamantakewa, da dai sauransu, Amurka tana fuskantar rauni, kuma ba za ta iya mallakar karfin da take da shi shekaru 20 ko 30 da suka gabata ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Tattaunawa da wannan gwamnatin Amurka bai kawar da takunkumin ba, a maimakon haka, ya dagula matsalar takunkuman, da kara matsin lamba, da bude kofa ga sabbin bukatu da buri.

A wani bangare na jawabin nasa, Imam Khamenei ya jaddada cewa gwagwarmaya a kasashen Palastinu da Lebanon ta kara karfi da himma fiye da yadda suke a da, yana mai cewa: Sabanin abin da makiya suke tsammani ba a durkusar da gwagwarmayar Palastinu da ta Labanon ba, sai dai sun kara karfi da kuzari. Eh, shahadar shugabanni ta jawo musu hasara Dan Adam amma hakan ya kara musu kwarin gwiwa”.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Mutum kamar Sayyid Hasan Nasrallah ya tashi cikin daukakar sama yana mai bacewa daga wannan taron, kuma ana jin hasarar rashinsa, to sai dai kuma a kwanakin da suka biyo bayan shahadarsa, ayyukan Hizbullah a kan yahudawan sahyoniya sun fi karfin wanda da ya gabata.

Dangane da gwagwarmayar Palastinawa kuwa Jagoran ya ce: A cikin gwagwarmayar Palastinawa mutane kamar shahidai Haniyyah, Sinwar, da Mohammed Deif sun tafi, amma duk da haka tsayin daka da gwagwarmaya na samun nasara, a tattaunawa da yahudawan sahyoniya da magoya bayanta da Amurka suka yi, na sanya sharuddan da suke da shi a daya bangaren.

Imam Khamenei ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da goyon bayan gwagwarmayar gwagwarmaya yana mai cewa: Jami'an kasar Iran da suka hada da gwamnati da shugaban kasar sun amince da wajibcin goyon bayan gwagwarmayar Palastinu da Lebanon gwargwadon iko. In sha Allahu al'ummar Iran za su ci gaba da rike tutar gwagwarmaya wajen fuskantar girman kai kamar yadda suka yi a baya”.

Jagoran ya kuma yi ishara da abubuwa daban-daban da suka faru a shekarar da ta gabata yana mai cewa: A irin wadannan ranaku na shekarar da ta gabata, shahidai Sayyid Raisi, Sayyid Hassan Nasrallah, Haniyyah, Sayyid Safiyuddin, Sinwar, Deif, da wasu fitattun masu fafutikar kare juyin juya hali sun kasance a cikinmu, amma yanzu ba su tare da mu, don haka ne makiya suke ganin mun raunana ne.

Jagoran ya ci gaba da jaddada cewa: “Duk da haka, ina mai tabbatarwa da cikakkiyar kwarin gwiwa cewa, duk da cewa rashin wadannan ‘yan’uwa masoya na nuni da babban rashi a gare mu, amma mun kara karfi a fagage da dama idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma a wasu wuraren ba mu yi rauni ko kadan ba.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya yi nuni da cewa, yunkuri na kyamar Amurka da daliban jami'a suka fara, irin su ranar "Azar 16" (December 7, 1953) da daliban jami'ar Tehran suka yi na nuna adawa da ziyarar Nixon, wanda ya kai ga kashe dalibai uku da gwamnati ta yi, ya samo asali ne sakamakon fallasa hakikanin yanayin kasashen yamma.

Hakazalika, Imam Khamenei ya yi nuni da irin yadda ake kara sha’awarar dogara ga kasashen yammaci, duk kuwa da irin koma bayan da suka samu kafin nasarar juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa, da a ce juyin juya halin Musulunci bai faru a shekara ta 1979 ba, da kasar nan ta hau hanyar da za ta kai ga dogaro da kasashen waje, wanda hakan zai hana ta samun duk wata fa'ida da wadatar ruhiyya”.

Jagoran ya kuma yi ishara da dagewar da ma'abota girman kan duniya suke yi na ci gaba da fada da makirce-makircen da suke yi kan juyin juya halin Musulunci yana mai cewa: "Suna cewa "mu ne farko," ma'ana wajibi ne dukkanin duniya su fifita maslaharsu fiye da nasu, wannan kame-kamen da suke yi a yau a bayyane yake ga kowa da kowa, yayin da Iran ta Musulunci ita ce kasa daya tilo da ta bayyana karara cewa ba za ta sanya maslahar wasu kasashe a karkashin wani maslahar ta ba a ko wane yanayi.

Haka nan kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi imani da cewa yunkurin makiya musamman ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa na zamani da nufin dawo da tasiri da iko da kasashen yammacin Turai kan Iran da kuma farfado da ruhin mika kai da mika wuya da kuma dogaro ga kasashen yammaci da wannan dabi’a ta yi galaba a tsakanin daliban jami'a na Iran kafin juyin juya halin Musulunci.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha