13 Maris 2025 - 02:31
Source: ABNA24
‘Yan Ta’adda Sun Kai Harin Ta'addanci Kan Jirgin Fasinja A Pakistan

Mayakan Balochistan Liberation Army (BLA) sun kai hari kan jirgin kasan Jaffar Express tare da tarwatsa layin dogo, inda suka kashe mutane 21 da dakarun tsaron Pakistan 4.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari kan wani jirgin kasa na fasinja a lardin Balochistan na Pakistan. Rahotanni daga kafafen yada labarai na nuni da cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da fasinjoji da dama.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan jirgin "Jafar Express" da ke tafiya daga Quetta zuwa Peshawar inda suka yi garkuwa da wasu fasinjoji bayan tsayar da jirgin.

A cewar majiyoyin labarai, an kai harin ne a yankin tsaunuka na Mach da ke lardin Balochistan, wanda ya raunata direban jirgin tare da tsayawa.

Rahotanni sun ce maharan sun fara lalata hanyar jirgin ne ta hanyar amfani da ababen fashewa sannan suka bude wuta. Kimanin fasinjoji 500 ne ke cikin jirgin, kuma wasu daga cikinsu sun samu raunuka sakamakon harin. Anci gaba da jin karar harbe-harbe a yankin, kuma tsoro da firgici ya ci gaba da mamaye fasinjojin.

Nan take jami’an tsaro suka kewaye yankin bayan sun samu rahoton faruwar lamarin inda suka aike da jami’an ceto zuwa wurin. An kuma sanya asibitocin da ke kusa da su cikin shirin gaggawa don karbar wadanda suka jikkata idan an bukata.

Sai dai saboda rashin kyawun wayar hannu a wurin da lamarin ya faru, yana da wuya a iya sadarwa da jirgin da fasinjoji.

Jami’an tsaro sun sanar da cewa an fara gudanar da ayyukan ceto fasinjoji tare da dawo da iko da yankin, kuma ana ci gaba da kokarin samun hadaka da ma’aikatan jirgin.

An kuma samu rahotanni a shafukan sada zumunta na cewa, kungiyoyin 'yan aware na Baloch ne suka kai wannan harin ta'addanci, inda suka ce wadanda aka yi garkuwa da su sojojin Pakistan ne.

Bayan kokari daga wajen jami’an tsaron kasar da kai ruwa rana an kawo karshen garkuwa da mutane a Pakistan tare da kashe duk 'yan ta'adda

Aikin ceto daruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su, ya fara ne bayan da wata kungiyar 'yan aware dauke da makamai ta yi garkuwa da wani jirgin kasan fasinja a wani yanki mai nisa na kudu maso yammacin Pakistan, inda aka kashe 'yan ta'adda 33 da 'yan ta'adda a nan take.

Mayakan Balochistan Liberation Army (BLA) sun kai hari kan jirgin kasan Jaffar Express tare da tarwatsa layin dogo, inda suka kashe mutane 21 da dakarun tsaron Pakistan 4.

Rundunar sojin Pakistan ta sanar da cewa ta kubutar da mutane 155 da aka yi garkuwa da su daga hannun 'yan ta'adda da suka kai hari kan wani jirgin kasa na fasinja a lardin Balochistan.

A cewar wannan rahoto, sojojin Pakistan sun kara bayani da cewa: A ci gaba da farmakin da ake kai wa wadanda suka kai harin ta'addanci kan wani jirgin kasan fasinja a lardin Balochistan, an kubutar da fasinjoji 155 da aka yi garkuwa da su, yayin da jami'an tsaro suka kashe wadanda su kai garkuwa da mutanen su 27.

Tun da yammacin ranar Talata ne dai ake ci gaba da kai hare-haren soji a yankin hamadar Bolan na lardin Balochistan bayan wani hari da wasu da dama da ke da alaka da kungiyar 'yan ta'adda da 'yan aware ta Baloch Liberation Army suka kai.

Rundunar sojin Pakistan ta yi nuni da cewa, 'yan ta'addan da suka hada da 'yan kunar bakin wake, sun yi amfani da fasinjojin jirgin a matsayin garkuwar mutane, don haka jami'an tsaro na gudanar da aiki tare da yin taka-tsantsan don hana cutar da fasinjojin.

A yayin da 'yan tawayen ke ikirarin cewa har yanzu suna da mutane 100 a hannunsu kuma har yanzu ana ci gaba da kai farmakin.

'Yan tawayen da ke neman ballewa daga kungiyar 'yan ta'adda ta Baloch Liberation Army sun dauki alhakin kai hari kan wani jirgin kasa na fasinja tare da yin garkuwa da fasinjojin sa.

Majiyoyin cikin gida sun yi ikirarin cewa sama da mutane 100 da ke cikin jirgin fasinjan na dakarun soji ne da ke dawowa daga wani aiki a lardin Balochistan kuma yanzu haka ‘yan tawayen ‘yan awaren ke garkuwa da su.

Firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai kan fasinjojin jirgin kasa a lardin Balochistan a cikin wani sako da ya aike da su inda ya ce: Za a ci gaba da murkushe masu aikata wannan ta'addanci har sai an kawar da 'yan ta'adda na karshe.

Dakarun sojin kasar sun yi nasarar kammala aikin daukin a yammacin ranar Laraba, inda suka kashe 'yan ta'addar tare da kubutar da dukkan fasinjojin cikin koshin lafiya.

Bayan wannan aikin, an sako mutane da dama da suka hada da mata da kananan yara... An gudanar da aikin na karshe cikin kulawa da inganci.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha