Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Dr.Syed Ebrahim Raisi a yammacin jiya Litinin a wata tattaunawa ta wayar tarho da iyalan shahidan tsaro Salman Amirahmadi ya bayyana cewa: Babban jarin kasar Iran ta musulunci su ne maza da mata Shahidai irinsu Amirahmadi. wadanda a lokuta daban-daban, suka fuskar kunci da hatsari daban-daban, su ka bada kawukansu don kar wani abunki ya sami kasa da alummarta.
A yayin da yake mika ta'aziyyarsa ga iyalan shahidi Amir Ahmadi, shugaban ya bayyana dabiun sadaukarwa da shahada daya amatsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da suke da shi na karfin kasa a kasar Iran, ya kuma kara da cewa: abubuwan da suka a sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke alfahari da samun nasara a fagen Gwagwarmaya tare da dukkan nau'ikan barazana, makirci da ayyukan makita, su ne, zamantakewar al'umma, hadin kai na kalma da dabia ta sadaukarwa ta shahada.
Raisi ya kira tsaro da ikon hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda irin matsayin al'ummar Iran da kuma kokarin dubban shahidai, sannan ya jaddada kokarin kowa na kare wannan babbar kasa.
A yayin da yake jaddada wajibcin bin diddigin shahadar Amir Ahmadi, Dakta Raisi ya bayyana matukar kokarin da dukkanin hukumomin da ke da alhakin aiwatar da wannan aika aika domin zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika da kuma masu kitsa hakan a kasar nan.
A karshe ya yaba da kokarin da dukkanin jami’an tsaron kasar nan ba dare ba rana suke yi na wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan, ya kuma bayyana cewa: In sha Allahu wannan kokari yana samu lada a gaban Allah Madaukakin Sarki.
342/