Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Alquraishi wanda asalain sunansa shi ne Juma Awan Al-badari ya karbi ragamar jagorancin kungiyar ta Isis ne tun bayan kashe tsohon shugabanta wato Abu Ibrahim Al’kuraishi, a wasu hare- hare da sojojin Amurka suka kai a kasar siriya a watan fabarerun da ya gabata.
Bisa bayanan da jami’an tsaron kasar Iraki suka fitar Badri shi ne dan uwan shugaban farko na kungiyar ta ISIS Abubakar Bagadadi wanda kungiyar suka kira da khalifa a garin mousen a shekara ta 2014.
Tashar Talabijin ta OdaTv ta rawaito cewa Jami’an yan sanda sun kama shugaban yan ta’addan ne bayan da aka dade ana sa ido a gidan da yake ciki, sai dai ba’ayi musayar wuta ba ko kadan alokacin kai samamen.
A yau Alhamis ce kungiyar ta ISIS ta sanar da alhakin harin bomb d aaka kai a garin Mazar I sharif dake Arewacin kasar, inda aka bayyana cewa akalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar.
342/