Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Mutane takwas ne aka rawaito sun suka mutu, kana wasu sama da 200 suka jikkata da suka hada da ‘yan sanda biyu, kana an farmawa gwamnan gine-gine ana ta kwasar ganima, tun fara rikicin mafi muni.
A halin da ake ciki dai masu bore a kasar suna neman shugaban kasar Gotabaya Raja-paksa da ya sauka daga mulki, wanda ke nufin murabus din da firaminsitan kasar ya yi bai gamsar da masu zanga zangar ba.
Firaministan kasar Mahinda Raja-paksa ya yi murabus ne bayan artabun da akayi tsakanin magoya bayansa da kuma masu zanga zangar ranar Litini.
342/