24 Afirilu 2022 - 16:42
Sojoji Masu Mulki A Guinea Sun Sallami Alpha Conde

Sojojin da suka kwace mulki a Guinea, sun sallami hambararen shugaban kasar da suke tsare da Alpha Condé.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Matakin sojin na sakin Mista Conde, na zuwa ne kwanaki uku gabanin wa’adin da kungiyar rara tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ta gindayawa sojojin na su sake shi, su kuma gabatar da jadawalin zabe domin mika mulki ga farar hula.

Saidai wasu ‘yan kasar na danganta matakin sojin da wani yunkuri na baiwa Alpha Conden wata damar sulalewa shari’a a kasar, yayin da ita kuwa tsahuwar jam’iyya mai mulki ta sanya sakin tsohon shugaban a matsayin sharadin shiga babban taron kasar.

A ranar 5 ga watan Satumban bara ne sojojin karkashin jagorancin Laftana kanal Mamadi Doumbouya, suka hambarar da mulkin shugaba Conde mai shakara 84.

342/