23 Afirilu 2022 - 18:36
Mutane 11 Ne Suka Mutu Wasu Kuma Suka Jikkata A Harin Bom Da Aka Kai Kasar Sumaliya

Rahotanni sun bayyana cea kimanin mutane 3 sune suka mutu wasu guda 11 kuma suka jikkata samakamon wani harin bomb da dan kunar bakin wake yakai a birnin Magadishu fadar mukin kasar Sumaliya a yammacin jiya Juam’a,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kakakin yan sandan birnin Abdilfatah Aden Hassan ya fadi cewa tuni aka garzaya da wadanda suka jikkkata zuwa Asibiti somin yi musu bagani bayan da jami’an tsaro sun shawo kan lamarin da dawo da doka da oda a inda harin ya faru a wajen dakin cin abinci wanda aka bude kwanannan a gabar teku ta Lido.

Wasu bayanai sun nuna cewa jam’ian tsaron da suka isa wajen da wuri sun taimaka wajen hana yan kungiayr Al’shabab da suke yi yunkurin kutsa kai har cikin dakin cin abincin bayan da bomb din ya fashe, jami’an tsaro sun ceto wani kwamishina yan sanda dake cikin dakin cin abinc tare da wasu mambobin majalisar kasar ta sumaliya su 11.

Yanzu haka dai an fara gudanar da bincike wanda ked a hannun wajen kai harin, yazuwa yanzu an tabbatar da kisan mutane 6 da jikkata wasu guda 7 sakamakon harin,

Kungiyar al shabab dake kai hare hare a gabashin Afrika ta sanar da alhakin kai hari na jiya tace mayakanta suna dakun manyan jami’an gwamnatin kasar ne.

342/